Ranar Hausa 2024: Muhimman Abubuwa 3 da za Su Amfani Hausawa
- A ranar 26 ga watan Agusta ake murnar ranar Hausa ta duniya inda Hausawa daga kasashe daban daban suke bikin ranar
- Hausawa su kan yi murnar ranar wajen yin rubutu da suka kunshi tarihi, karin magana da sauran abubuwa da suka shafi harshen
- Legit ta tattauna da wata matashiya mai suna Salamatu Ibrahim domin jin ko ta dauki darasi a ranar Hausa ta wannar shekarar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - A duk ranar 26 ga watan Agusta Hausawa a fadin duniya na murnar Ranar Hausa inda suke gabatar da abubuwa kala kala.
Haka zalika a wannar shekarar Hausawa da dama sun yi rubutu a kafafen sadarwa domin murnar ranar Hausa ta 2024.
A wannan rahoton, mun tattaro muku rubutu guda uku masu muhimmanci da wasu daga cikin Hausawa suka wallafa domin murnar ranar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin Ranar Hausa a Musulunci
Malami a jami'ar Ahmadu Bello kuma jagora a Darul Hadis da ke Zariya, Dr Kabir Abubakar ya yi rubutu kan hukuncin Ranar Hausa a Musulunci.
Dakta Kabir Abubakar ya bayyana cewa Ranar Hausa ba a ware ta bane domin wani biki na addini da ake nufin samun lada.
Saboda haka ya wallafa a Facebook cewa za a iya daukar Ranar Hausa kamar ranakun da ake warewa domin zaburar da jama'a kan muhimmaci wani abu wanda babu laifi a cikin hakan.
Koyon ka'idojin rubutun Hausa
Wani Bahaushe Malami a kasar Jamus, Dr Muhsin Ibrahim ya yi kira ga Hausawa kan koyon ka'idojin rubutun Hausa saboda muhimmancin hakan.
Dr Muhsin Ibrahim ya wallafa a Facebook cewa yana da muhimmanci Hausawa su dage ta inda kafin ranar Hausa ta shekara mai zuwa sun koyi ka'idojin rubutun.
Tunani kan 'Sai bango ya tsage'
Wani likita a jihar Adamawa, Dr Raji Bello ya yi kira ga Hausawa ne kan zurfafa tunani a kan karin magana da ke cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun kofar shiga.
Dr Raji Bello ya wallafa a Facebook cewa ya kamata Hausawa su yi dubi ga karin maganar domin neman hanyoyin magance matsalolin Arewacin Najeriya.
A bisa hasashe, Likitan ya fadi haka ne kasancewar da yawa daga cikin matsalolin Arewa daga yankin aka haddasa su.
Legit ta tattauna da Salamatu
Wata matashiya mai suna Salamatu Ibrahim ta tabbatarwa Legit cewa za ta yi aiki da kiran da aka yi na koyon ka'idojin Hausa.
Salamatu ta ce ko da kadan kadan ne za ta rika koyo domin samun kwarewa kafin shekara mai zuwa.
Sarkin Kano ya yabi Abba Kabir Yusuf
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha ruwan kalaman yabo kan kula da 'yan fansho da kuma inganta ilimin yara mata.
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne ya yi wannan yabon yayin da ya gana da wasu kwamishinonin Kano a fadarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng