Aljannar Duniya: Bidiyon Tamfatsetsen Gidan Wizkid na Landan ya Ja Hankalin Jama’a

Aljannar Duniya: Bidiyon Tamfatsetsen Gidan Wizkid na Landan ya Ja Hankalin Jama’a

  • Bidiyon fitaccen mawakin Najeriya Wizkid yana zagayawa a wani katafaren gidansa da ke Landan ya jefa mutane cikin tsananin mamaki
  • Katafaren gidan alfarmar ya jawo ce-ce-ku-ce daga magoya bayan mawakin, inda wasu suka yabawa mawaƙin na shuka bishiyoyi a gidan
  • A wani faifan bidiyon, an ga Bolu, dan Wizkid yana nuna kwarewarsa a buga kwallon kafa da kwallon kwando a wani bangare na gidan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sunan fitaccen mawakin Najeriya, Ayo Balogun (Wizkid) ya sake shiga cikin wata tattaunawa da ta dauki hankula a shafukan sada zumunta.

Wani faifan bidiyo na gidan mawakin na Landan da ya bazu a kwanan nan a yanar gizo ya bar mutane cikin tsananin al'ajabin irin girma da kuma kawatuwarsa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama boka da ake zargi yana tsafi da kashin ɗan Adam

Mutane sun yi magana kan irin girman gidan Wizkid da ke Landan
Wani bidiyo na gidan Wizkid a Landan ya bazu a yanar gizo. Hoto: @wizkidayo/@olamide0fficial
Asali: Instagram

An ga bidiyon katafaren gidan Wizkid

Bidiyon katafaren gidan wanda wani @OlamideOfficial ya wallafa a shafinsa na X ya dauki hankalin mutane da yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, an hango mawaki Wizkid yana tare da abokai da 'yan uwa a cikin katafaren lambun sa da ke cikin gidan wanda shi ma ake kyautata zaton zai iya daukar wani ginin.

Daya daga cikin abubuwan da suka ja hankali shi ne lokacin da aka ga dan Wizkid, Sihiyona, ya na guje-guje a cikin gidan a lokacin da ake daukar bidiyon.

Yaron Wizkid ya nuna kwarewa a kwallo

A wani faifan bidiyon na daban wanda Tooexclusive ya wallafa a Instagram, an kuma hangi dan Wizkid na fari, Boluwatife, yana buga kwallo da abokansa a cikin lambun gidan.

'Yan Najeriya sun gaza danne abin da ke ransu, sai da suka yabawa kokarin Bolu na taka leda da kuma kwarewarsa a wasan kwallon kwando.

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Tinubu ya dawo biyan al'umma tallafi, an ci moriyar arzikin kasa

A cikin bidiyon, an ga Bolu ya kara da cewa yana jin kansa kamar Cristiano Ronaldo (CR7).

Dubi bidiyon katafaren gidan Wizkid a nan kasa:

Mutane sun yi ce-ce-ku-ce kan gidan Wizkid

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin da Legit Hausa ta tattara kan tamfatsetsen gidan Wizkid.

@thatbobpr:

"Girman wannan gidan har ya zarce ginin Aafin Olubadan."

@Mautiin01:

"Wannan ai aljannar duniya ce."

@zxenergyy:

"Kun ga aikin kudi masu gidan rana."

@OladmejiAkogun:

"Filin shakatawar gidan wani a Landan ya kusa girman wani kauye a Ijebu."

@dholly_pee_xs:

"Ni da ma ina zargin uban zai tsaya a waka, yaron kuma ya zama dan kwallo."

@mazijudepondis8:

"Arziki ta ko ta ina. Uba yana waka, dansa yana buga kwallo. Haba, ashe dole 'ya'yan manya su rika yin nasara a rayuwa."

Wizkid da mawaka 10 mafi arziki a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Wizkid shi ne mawaƙin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya bayan ya mallaki kuɗin da ya kai sama da dala miliyan 30 (Naira biliyan 44.6) a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi kuskure, akwai ma'aikatan da ba za su samu albashin N70,000 ba

P-Square, (Peter Okoye (Mr.P) da Paul Okoye (Rudeboy), su ne ke bin bayan Wizkid a jerin mawaka mafi kudi a Nigeria bayan da suka mallaki dalar Amurka miliyan 27.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.