Cika Shekaru 10: Tashar Arewa 24 Ta Kawo Zafafan Shirye Shirye 3

Cika Shekaru 10: Tashar Arewa 24 Ta Kawo Zafafan Shirye Shirye 3

  • A watan Yunin wannar shekarar tashar talabijin din Arewa 24 ta yi bikin cika shekaru 10 da fara yaɗa shirye shirye a jihar Kano
  • Biyo bayan haka, tashar ta fitar da sababbin shirye shirye guda uku domin bunkasa alakarta da al'umma Arewacin Najeriya
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku jerin shirye shiryen da yadda za su rika gudana a tashar talabijin din Arewa 24

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - A watan Yunin wannan shekarar ne gidan talabijin din Arewa 24 ya cika shekaru 10 da kafuwa.

Mataimakin shugaban tashar, Celestine Umeibe ya sanar da wasu sababbin shirye shirye da suka kawo bayan cika shekaru 10.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya tsallake rijiya da baya, iyalansa 3 sun mutu a gobara

Arewa 24
Arewa 24 ta kawo sababbin shirye shirye. Hoto: Arewa24
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku jerin sababbin shirye shiryen kamar yadda Celestine Umeibe ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sababbin shirye shiryen Arewa 24

1. Shirin Arewa Gen-Z

Rahoton Daily Trust ya ce tashar Arewa 24 ta sanar da fara shirin Arewa Gen-Z da zai rika mayar da hankali ga matasan Arewacin Najeriya,

Tashar ta bayyana cewa shirin zai kasance na mintuna 30 duk mako kuma zai rika zakulo labaran mutanen da suka yi zalaƙa domin su karfafi matasa masu tasowa.

2. Shirin Jaru Road

Tashar Arewa ta bayyana cewa za ta fara shirin Jaru Road da zai rika kawo yadda lamura suke gudana a Arewacin Najeriya amma da harshen Turanci inji Punch.

A cewar tashar, shirin zai yi kokarin fadakar da mutane a nahiyar Afirka dama duniya baki daya kan yadda rayuwa ta ke a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

3. Shirin Climate Change Africa

Haka zalika, tashar Arewa 24 ta fitar da sabon shiri dai zai rika mayar da hankali kan yadda dumamar yanayi ke tasiri a yankin Arewa.

Mataimakin shugaban tashar Arewa, Celestine Umeibe ya ce wannan kokari da suke na nuna yadda suka damu da mayar da hankali kan al'ummar Arewacin Najeriya da cigabanta.

Shiga fim: Hadiza Gabon ta shawarci mata

A wani rahoton, kun ji cewa fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta ba yan mata masu shirin shiga harkar fim shawarar hakuri a kan shi ya fi alheri.

Hadiza Gabon ta fadi haka ne tare da bayyana cewa akwai tarin illoli ga 'yan mata idan suka shiga masana'antar Kannywood domin fara fim.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng