Dogo Mai Dogon Zamani: Bidiyon Zankalelen Yaro Dan Aji 4 a Firamare ya Dauki Hankalin Jama'a

Dogo Mai Dogon Zamani: Bidiyon Zankalelen Yaro Dan Aji 4 a Firamare ya Dauki Hankalin Jama'a

  • Bidiyon wani dogon yaro ya karade shafukan sada zumunta bayan an wallafa shi a shafin Tiktok domin nuna irin tsayin da Allah ya yi masa
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta na ta mamakin shekarun zankalelen yaron, musamman bayan an bayyana cewa ajinsa 4 a Firamare
  • Duk da dai ana hasashen yaron ya cikin shekarunsa na goma sha, amma ba a fadi adadin shekarunsa ba wanda hakan ya kara daukar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

South Sudan- Bidiyon wani yaro wanda har yanzu ba a bayyana shekarunsa ba ya dauki hankali matuka saboda matukar tsayi da ya ke da shi.

Kara karanta wannan

Badakalar N33bn: An samu matsala a kotu bayan Ministan Buhari ya fadi ana shari'a

Tuni masu amfani da shafukan sada zumunta su ka yi ta magantuwa kan irin baiwar tsayin yaron, yayin da wasu ke ganin abin da mamaki.

Dogon Yaro
Bidiyon dogon yaro ya dauki hankalin jama'a Hoto: dantez_305
Asali: TikTok

A wani bidiyo da wani mai amfani da shafin zamani na Tiktok ya wallafa a dantez_305, ya ce wannan shi ne yaro mafi tsayi da ya gani a ranar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan wace kasa ce yaron?

Duk da ba a fadi takaimaimai garin da yaron ya fito ba, an bayyana cewa dan kasar Sudan ta Kudu ne da ke Afrika ta Gabas inda aka san su da dogayen mutane.

Tuni aka fara tunanin zankalelen yaron dan kabilar Dinka ne wadanda Allah (SWT) ya yi masu baiwa da matukar tsawo, Legit.ng ta wallafa.

Masu amfani da shafin Tiktok da su ka kalli bidiyon sun ce ba su taba ganin dogo haka ba, yayin da wasu daga kasar Sudan su ka ce ai wannan ba abin mamaki ba ne.

Kara karanta wannan

Bidiyon magidanci kwance share share a bayan mace tana tuka babur ya jawo cece kuce

Ga abin da wasu masu amfani da Tiktok ke cewa @TONDAH ya ce:

"Babu wanda ke maganar kwanon abincin da ya rike.

@Shabba ya ce:

"Ta yiwu ku ji a abin yara ya ke kuma shekarunsa biyar.

@Lyn ya ce:

Kuma ci gaba da girma ya ke, ku tuna kila ajinsa 3.

Bayan magidanci a babur ya dauki hankali

A wani labarin kun ji cewa an gano bidiyon wani maganci kwance a bayan wata mata ta na tuka shi a kan babur, shi kuma ya na bacci.

Mutane su na mayar da martani kan bidiyon, yayin da wasu ke ta ihu idan ta zo wucewa ta inda su ke, shi kuma magidancin ko a jikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.