‘Yar Najeriya Mai Koyarwa a Japan Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Dalibai Na Kiranta da Suna ’Biri’

‘Yar Najeriya Mai Koyarwa a Japan Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Dalibai Na Kiranta da Suna ’Biri’

  • Wata budurwa 'yar Najeriya wacce ke aiki a matsayin malamar makaranta a Japan ta koka game da nuna banbancin launin fata
  • Malamar makarantar ta bayyana abinda take fuskanta inda dalibanta kai tsaye babu kunya suke kiranta da suna Biri
  • Tuni jama'a suka bazama yi mata martani inda wasu ke ganin babu dalilin sharbar kuka yayin da wasu ke nuna mata goyon baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Japan - Wata malamar Najeriya a kasar Japan mai amfani da sunan @gamezu3, ta koka a kafar sada zumunta kan kalaman wariyar launin fata da dalibanta ke furta mata.

A wani bidiyon da ta wallafa a shafinta na TikTok malamar makarantar ta fashe da kuka yayin da ta tuna irin wulakancin da take fuskanta.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur ta tsananta a Najeriya, NNPC zai nemo sabon rancen dala biliyan 2

Dalibai na kiran malama 'yar Najeriya biri a Japan
'Yar Najeriya mai koyarwa a Japan ta ce dalibanta biri suke kiranta, ta fashe da kuka a bidiyo. Hoto: @gamezu3
Asali: TikTok

"Yar Najeriya ta fashe da kuka a bidiyo

'Yar asalin Najeriyar, wacce ta kammala karatunta daga jami'ar Japan, ta wallafa a shafinta na TikTok din cewa dalibanta na kiranta da Biri saboda nuna kaskanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta koka a game da irin cin kashin da take fuskanta, da kuma yadda ta gaji da rayuwar ketare. Kalaman da ta rubuta a kan bidiyon da ta wallafa sune:

"A wannan ranar, dalibaina sun kira da suna Biri tare da kalmar N! Wannan rayuwar ketaren na gaji da ita! #AGyaraAfrika."

Tuni bidiyon ya ballo kace-nace daga jama'a ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamanin. Ga bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan koken malamar

Mrs A ta ce:

"Dariya mai yawa. Ai martani zan musu da Yarabanci in ce awon iran é ni biri. Ban ga dalilin yin kuka kan irin wannan karamin abun ba.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

Gerald ya ce:

"Daga nesa ba za ka fahimci takaicin nuna banbancin launin fata ba har sai an yi maka. Akwai takaici, musamman idan shi ne karon farko."

Alex d black guy ya ce:

"Wannan abun akwai kunar rai, yanda ma take kukan ne ya bata min rai."

Virtue Samuel ya ce:

"Jiya wani ya tambayeni, a kasarmu akwai zaki? Nace masa ce eh kuma gado daya muke kwana da macijina. Har yanzu tsoro na yake."

Brenda ta ce:

"Wannan ne yasa a matsayinmu na 'yan Kenya muke son gyara kasar mu. Bamu son zuwa ketare saboda zamu iya gyara kasarmu. Ana iyawa, sauran 'yan Afrika su yi hakan suma."

An kama kurar da ta tsere a Jos

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa hukumar kula da gandun dabbobin Jos a jihar Filato ta bayyana cewa an kamo kurar da ta tsere daga gidan.

Shugaban gidan ne ya sanar a wata takardar da ya fitar inda yace sai da aka yi mata allurar bacci ne aka samu damar damketa tare da mayar da ita keji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.