Saurayi ya rusa katafaren gidan da ya ginawa budurwarsa saboda ta rabu da shi
- Maza sun fusata, sun kfara kwace abubuwan da suka baiwa yan matansu idan suka rabu
- Da farko an samu labarin masu kwace kaya da takalma
- Yanzu ga wani ya rusa giga gaba dayanta saboda budurwar ta yaudaresa
Wani matashi a shafin ra'ayi da sada zumunta na Tuwita ya bayyana yadda wani attajiri ya kai buldoza ya rusa katafaren gidan da ya ginawa budurwarsa.
A cewarsa, wannan abu ya faru ne a kasar Afrika ta kudu.
A bidiyon da ya shahara yanzu, @THAB4NG ya bayyana cewa attajirin ya yanke shawarar rusa gidan ne saboda budurwar ta rabu da shi.
Yace: "Wani attajiri ya kawo buldoza da TLB domin rusa gidan da ya ginawa budurwarsa bayan ta rabu da shi."
KU DUBA: Gwamnan Ondo ya sha alwashin dawo da Gwamna Obaseki APC bayan watanni 8 kacal a PDP
Kalli bidiyon:
DUBA NAN: Gwamnatina za ta agaza wa matasa miliyan ɗaya a kowacce shekara
A wani labarin kuwa, wata budurwa 'yar Najeriya ta kammala digirinta inda ta zama cikakkiyar likita kuma ta sanar da hakan cike da farin cikin wannan nasarar.
Babu kakkautawa kuwa ta wallafa hotunanta har uku a shafinta na Twitter mai suna @__Marryaam sanye da kayan likitoci.
"Daga karshe, na zama cikakkiyar likita... an dauka hoton da waya kirar iPhone 13," ta wallafa.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng