"Me Wadannan Mutanen Ke Mayar da Musulunci?”: Malamin Islama Da Ke Ikirarin Mu’ujiza Ya Sha Suka

"Me Wadannan Mutanen Ke Mayar da Musulunci?”: Malamin Islama Da Ke Ikirarin Mu’ujiza Ya Sha Suka

  • Mutane sun fara yin martani kan wani fai fan bidiyo da ya fara yawo a kafofin sada zumunta na wani malamin addinin Musulunci da ke warkar da wata gurguwa
  • Sanusi Lafiagi, wani malamin jami'a, wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na sada zumunta, ya yi Allah wadai da irin abin da malamin ya ke nuna wa.
  • Da yawa daga masu sharhi kan bidiyon, sun yi Allah wadai, yayin da wasu ke ganin hakan kawai hanyar damfara ce, kamar yadda ta taba faruwa a Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bidiyo ya nuna wani malamin Addinin Musulunci ya na nuna mu'ujizarsa yayin da ya ke kokarin warkar da wata gurguwa wacce ya rike ta a cikin masallaci, sauran mutanen da ke wajen na ambatar sunan Annabi Isa. Annabi Isah shi ne aka sani da Jesus a addinin Kirista.

Kara karanta wannan

Bidiyon wani mutum da ya juye galan din man ja a injin mota ya girgiza intanet

Ikirarin cewa kana da mu'ujiza ta warkar da wani ko yin wani abu wanda Allah ne kawai ke yi ya saba wa addini da al'adar musulmi, don haka ne ma da yawan wadanda suka yi sharhi a kan bidiyon suka yi Allah wadai da abin da malamin ya yi.

Malamin bogi
Ana ci gaba da caccakar wani malami mai karyar mu'ujiza Hoto: Sanusi Lafiagi
Asali: Twitter

Wani malamin jami'a, Sanusi Lafiagi, wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter, ya tambaya, "Shin me mutanen nan ke son mayar da addinin Musulunci ne?"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan Nigeria suka yi martani kan mu'ujizar malamin

Adedayo Onasanya ya bayyana cewa:

Ina karyar take a nan?
Annabi Muhammad (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya dade da sanar da mu irin alamomi na zuwan tashin alkiyama. Kowa ya san wadannan alamomin wadanda idan suka gama bayyana, to karshen duniya ya zo.

Kara karanta wannan

Likitoci sun yanke wa jarumin fina-finan Najeriya kafa don ceto ransa

"1. Bayyanar manzanni da malaman karya."
"2. Yawaitar cututtukan da mutane ba su san su a baya ba."
"3. Karancin ilimi da yawaitar jahilci, ma’ana jahiltar addini."
"4. Yawaitar kashe kashe ba tare da wani haddi ba."
"5. Dauke amana, ma'ana masu amana za su yi karanci."
"6. Neman ilimin addini domin yin kasuwanci da shi, da dai sauran su."

Idris Oni ya ce:

"Wannan damfara ce kawai."
"Da yawa mata ne ke fadawa komar irin wadannan malaman. Akwai wani malami shi ma da ya taba zuwa yankinmu, yana ikirarin shi jikan Bulala ne, yana warkar da mutane. Haka ya damfari mutane tare da yi wa mata da yawa ciki, ya gudu."
"Allah kadai ke da ikon warkar da marasa lafiya."

Adebayo Salami ya yi kira ga shuwagabannin addinin Musulunci na jihar Oyo da su dauki mataki akan lamarin, kamar yadda jaridar Legit ta ruwaito, inda ya ke cewa:

Kara karanta wannan

Bidiyon wani dan siyasa a Arewa ya sha kunya yayin kaddamar da rijiyar burtsatse, babu ruwa

"Magana ake akan addinin Musulunci."
"Ina fatan majalisar malamai ta jihar Oyo za ta dauki mataki akan wannan malamin."

Khalifa ya ce alamomi hudu da suka nuna ba musulmai ba ne.

"Sun shiga inda suke ikirarin masallaci ne sanya da takalma ga kuma kujeru."
"Logbara Isah" da karfin ikon issa?"
"Sautin kida na tashi da kuma wakoki"
"Wadannan 'yan damfara ne kawai masu neman na abinci"

Wani mutumi ya yi da'awar annabta a kasar Sudan

Ko a shekarar 2017, jaridar Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wani mutumi mai suna Abdulwahid Muhammad Nur a can kasar Sudan ya ce wai shi ma annabin Allah ne kuma ubangiji ya turo sa ga mutanensa.

Ya ce ana yi masa wahayi kamar dai annabawan Allah kuma tuni har an sauko masa da wata sura mai suna Sural Darfur, watau ta mutanen garin Darfur da ke kasar Sudan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel