An kama fasto a Abuja da yake sayar da man shafawa naira miliyan daya kwalba daya

An kama fasto a Abuja da yake sayar da man shafawa naira miliyan daya kwalba daya

- A ranar Asabar da ta gabata ne hukumar ‘yan sanda ta cafke wani fasto a Abuja

- An kama faston ne da laifin siyar da man waraka ga mutane a kan naira miliyan daya kowacce kwalba

- A cewarshi, wannan man zai iya warkar da cuta kowacce iri, samar da arziki mai yawa cikin wata daya, tada matacce tare da wasu mu’ujiza kala-kala

A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama shugaba kuma wanda ya kirkiro Jesus Deliverance Ministry dake Abuja, Fasto Shola Akande, wanda ake zargi da siyar da man waraka ga mambobin cocinshi a kan naira miliyan daya kowacce kwalba.

Kamar yadda faston ya bayyana, wannan man zai iya mayar da talaka futik hamshakin mai arziki a cikin wata daya tak, zai iya warkar da mutum kowanne ciwo, zai iya tada matacce kuma yana bayyana alamu tare da wasu mu’ujiza kala-kala.

Ya kara da cewa bai tirsasa kowa ya siya ba, amma ra’ayi ne. Duk kuwa wanda ya siya zai samu riba fiye da sau dari a kan yadda ya siya.

KU KARANTA: Hotuna: Jaruman Kannywood 11 da suke da mabiya mafi yawa a Instagram

Da yawa daga Kiristocin Najeriya sun soki wannan lamarin, sun kuma bayyana cewa siyar da man waraka bashi da matsuguni a littafin bibul. Babu inda wannan ‘ma’aikin’ ya ga hakan a bibul.

Kamar yadda wani daga cikin mambobin cocin ya bayyana, wasu mutanen har kwalba biyu suke siya. Wasu kuwa suna siyan fiye da hakan don amfaninsu da na abokansu.

Faston na daya daga cikin fastoci masu matukar arziki a Najeriya, yana samun sama da miliyan 20 a kowacce ranar Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng