Sallah: Hukumar Tace Fina Finan Kano ta Kafa Kwamitin Tsaftace Ayyukan Gidajen Wasanni
- Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano ta kafa kwamitin tsaftace shagulgula a gidajen wasanni yayin bukukuwan sallah
- Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ya kafa kwamitin ne domin ganin gidan wasannin ba su gudanar da wasannin da za su ci karo da addini ko al'ada ba
- Kwamitin, wanda aka kafa a yau Litinin zai bibiyi gidajen wasannin da kuma kai rahoto ga hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jiha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano - Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano ta kafa kwamiti na musamman wanda zai lura da yadda gidajen wasanni a Kano suka gudanar da shagul-gulan bikin karamar sallah.
Jami'in Hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya tabbatarwa legit Hausa cewa hukumar, Abba El-mustapha ne ya kaddamar da kwamitin a yau Litinin karkashin jagoranci daraktan kudi da mulki na hukumar, Abdulkarim Badamasi.
El-Mustapha ya ce an kafa kwamitin ne domin tabbatar da bin doka da dakile duk wani abu da ake tunanin zaici karo da al'adah ko tarbiyar addinin musulunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba El-mustapha a cikin sanarwar ya ce:
"Aikin kwamitin shi ne zagayawa gidajen wasannin domin lura da su tare da kawowa Hukumar rahoto kan yadda suka gudanar da shagulgulan bikin sallar."
Hukumar fina-finai ta ja kunnen kwamitin
Abba El-Mustapha ya kuma yi kira ga wanda aka zabo a matsayin yan kwamitin su mayar da hankali a kan aikin da aka ba su.
Ya hore su da kawo rahoton da ake bukata domin tsaftace ayyuka gidajen wasannin.
Kano: Za a hukunta wanda ya karya doka
Abba El-mustapha ya lashi takobin tabbatar da an hukunta duk wani gidan wasan da aka samu da laifin karya doka.
Daga cikin hukunce-hukuncen fa gidajen wasannin da aka samu da laifi za su iya fuskanta akwai ƙwace lasisin sa na dindindin.
Hukumar fim ta hukunta mai saɓa doka
A baya, kun ji hukumar ta dakatar da jarumin finafinan kannywood, Abdul Saheer na shekaru biyu saboda sabawa dokoki da ka'ida.
An zargi wannan tauraro da wallafa bidiyo mai ɗauke da batsa a shafukansa na sada zumunta wanda hakan ya jawo abin magana.
Asali: Legit.ng