Dan Daudu Bobrisky Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ya Son Ƙulla Wata Alaƙa Da Abokai

Dan Daudu Bobrisky Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ya Son Ƙulla Wata Alaƙa Da Abokai

  • Shahararren ɗan daudun nan da ya canja halittar sa zuwa ta mata Idris Bobrisky ya bayyana dalilin da ya sa ba ya ƙulla alaƙa da abokai
  • Ya bayyana cewa saurayinsa ya gargaɗe shi sannan kuma ya ba shi shawara kan hakan domin ya samarwa kansa zaman lafiya
  • Ya kuma bayyana cewa ya sha baƙar wahala sosai a hannun abokan da ya yi mu'amala da su a can baya, hakan ya sa ya ƙara kiyayarsu

Shahararren ɗan daudun nan Okuneye Idris Olanrewaju wanda aka fi sani da Bobrisky, ya bayyana dalilin da ya sanya baya wata alaƙa ta abokantaka.

Bobrisky, matashin da ke shiga irin ta mata ya ce bai ji daɗin abokan da ya yi ba, ya ce bai ji daɗin dangantakarsa da su ba.

Bobrisky
Dan Daudu Bobrisky Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ya Son Ƙulla Wata Alaƙa Da Abokai. Hoto: Miss Petite Blog
Asali: UGC

Mutane na yawan tuntuɓarsa

Kara karanta wannan

“Na Haɗa Kayana Na Bar Gidan": Wani Magidanci Yayi Fushi Ya Bar Matarsa Bayan Da Surukarsa Ta Dawo Gidansu

The Nation ta yi rahoto cewa Bobrisky ya ce mutane da dama na yawan tuntuɓarsa domin ƙulla alaƙa, amma sai ya ƙi basu dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba ya da sha’awar tarayya da wani saboda saurayinsa ya riga da ya gargaɗe shi kan cewa kada ya yi abota da kowa.

Bobrisky wanda kuma fitacce ne a shafukan sada zumunta ya yi wannan bayani ne a wani ɗan gajeren bidiyo da ya ɗora a shafinsa na Fesbuk cikin 'yan kwananin nan.

Ya ce mutane da dama kan kirashi, wasu na tambayar inda ya ke, wasu kuma na kiran ya zo su ɗan fita yawon shaƙatawa da sauran makamantansu.

Sai dai Bobrisky ya ce yanzu duk ba ya buƙatar ƙulla wata alaƙa da wani banda saurayinsa. Ya ce abokan da ya yi tarayya da su a baya sun wahalar da shi sosai.

Kara karanta wannan

Bautar Ƙasa: Bai Kamata Shirin NYSC Ya Zama Wajibi Ba, Farfesa Jega

A cewar Bobrisky:

“Mutane na yawan kirana suna maganganu irin, ‘ya ne Bobrisky, zo mu fita yawon shaƙatawa, kana Abuja ne.’ Yi hakuri, ba za mu iya fita shaƙatawa ba… Ba na son abokai yanzu. Abokai sun nuna min Shege.”

Saurayina ya gargaɗe ni, Bobrisky

Bobrisky ya kuma ƙara da cewa saurayinsa ya gargaɗe shi kan cewa ya ƙyale duk wata alaƙa da wani aboki, ya yi rayuwarsa ba tare da takura ba.

A faɗarsa:

"Saurayi na ya gargaɗe ni cewa, ba na da buƙatar wasu abokai. Ya ce in zauna a ɗakina. Ni kaɗai nake zaune a ɗakina. Ina son na zauna lafiya. Don haka, ina mai bada haƙuri ga mutanen da na ƙi karɓar tayin abokantaka da su. Ba alfahari nake yi ba, Ina so na samu kwanciyar hankali ne kawai.”

Ya kuma ƙara da cewa ya na da kyau ya san dalilin da ya sa mutum ya ke son ƙulla alaƙa da shi kafin ma ya iya karɓar abokantakarsa.

Kara karanta wannan

"Budurwa Daya Matsala": Matashi Mai Soyayya Da 'Yanmata Biyu Ya Nuna Su, Bidiyon Ya Dauki Hankula

Ma'aurata sun gano cewa su 'yan uwa ne na jini bayan tsawon lokaci

A wani labarin na daban kuma, wani miji da matarsa sun gano cewa su 'yan uwa ne na jini bayn shafe shekaru goma a tare.

Ma'auratan 'yan kasar Amurka sun bayyan hakan ne a wani bidiyo da suka dora a kafar sada zumunta ta TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel