Bayan Shafe Shekaru 10 Suna Cin Soyayya, Mata Da Miji Sun Gano Yan Uwa Ne Na Jini

Bayan Shafe Shekaru 10 Suna Cin Soyayya, Mata Da Miji Sun Gano Yan Uwa Ne Na Jini

  • Wasu ma'aurata sun jefa mutane cikin rudani bayan binciken kwakwaf da ya gigita su na neman raba alakarsu ta aure
  • Bayan kwashe shekaru 13 suna murza soyayya kuma sun yi aure shekara 10 baya, ma'auratan sun gano cewa su 'yan uwan juna ne na jini
  • An samu ra'ayoyi mabambanta game da Bidiyon gaskiyar da ma'auratan suka gano, wasu na ganin sun baro shiri tun rani

Wasu ma'aurata da suka shafe shekaru 10 da yin aure sun gano gaskiyar da ta gigita su, watau sun kasance 'yan uwa na jini.

Ma'auratan yan asalin kasar Amurka sun bayyana abinda suka gano da ya kaɗa hanjinsu a wani Bidiyo da shafin @stzyathletemo ya wallafa a TikTok.

Rigimar aure.
Bayan Shafe Shekaru 10 Suna Cin Soyayya, Mata Da Miji Sun Gano Yan Uwa Ne Na Jini Hoto: @stzyatletemo
Asali: UGC

Mijin wanda ya yi bayani a madadin iyalinsa ya ce sun shiga daga ciki ne a shekarar 2008 kuma sun haifi dansu na fari a shekarar 2011.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

A shekarar 2015, Magidancin ya bayyana cewa abokiyar rayuwarsa ta sake haihuwar dansu na biyu kuma sun shafe shekaru 10 kenan suna tarayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai a halin yanzun, ya bayyana cewa a 'yan kwanakin nan suka gano cewa su yan uwa ne na jini.

Kalli bidiyon anan

Yadda mutanne suka bayyana ra'ayoyinsu kan batun

Kevinellis211 ya ce:

"Wannan ya zama ruwan dare fiye da tunanin ku, ina da wasu abokai da suka yi aure, kwanan na suka gano ashe wa da ƙanwa ne na jini."

Ashley Blanks ta ce:

"Mamata da ta dauke ne a matsayin ɗiyarta ta gargade ni kana na yarda na kulla alaka da wani ta wayar tarho saboda mahaifina na da 'ya'ya barkatai a gari."

Marzeitaly yace:

"Wannan ya sa yanzu akwai bukatar mutane su bincika sosai kan asalinsu saboda a baya iyaye sun yi shegantaka yadda suke so kuma komai a rufe yake ba wanda ya sani."

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano

A wani labarin kuma mun kawo maku Yadda Wani Mutumi Ya Gigita Diyarsa Yayin da Ya Shiga Dakin Tsohuwar Matarsa Ya Tube Kaya

Lamarin dai ya auku ne kwanaki kadan bayan mutumin sa saki matarsa, kawai yarinyar ta shirya masu shagalin kara zumunci kuma ta gayyaci mahaifinta.

Sai dai da zuwa magidancin kawai sai gani aka yi ya fara cire tufafin dake jikinsa a wani bidiyo da aka wallafa a Soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel