"Na Tuba Ba Zan Kara Ba", Matashi Ya Koka Bayan Ya Sanya N400k na Mahaifiyarsa a Caca, Sun Bace Bat

"Na Tuba Ba Zan Kara Ba", Matashi Ya Koka Bayan Ya Sanya N400k na Mahaifiyarsa a Caca, Sun Bace Bat

  • Wani matashi ɗan Najeriya, ya buƙaci da a kawo masa agaji ya samu ya biya kuɗin mahaifiyarsa N400k, da ya yi asarar su a caca
  • Matashin ya ce ya rasa abinda ke masa daɗi domin mahaifiyar sa na buƙatar kuɗin saboda tafiyar da za ta yi yau ranar Laraba
  • Ɗalibin wanda a baya ya daina caca, ya bayyana dalilin da ya sanya ya sake dawowa ruwa, sannan ya sha alwashin kiyayar ta gaba ɗaya

Wani ɗalibi ɗan Najeriya mai shekara 26, mai suna Tomiwa Olaniyan, ya koka a shafin sa na Twitter, bayan ya yi asarar kuɗin mahaifiyarsa, N400k a caca.

A wani rubutu da ya yi wanda yanzu ya goge shi, Tomiwa wanda ya ke amfani da sunan @tomiwa201, ya roƙi wani mai siyar da littattafai, @Mrbankstips taimako, inda ya ce mahaifiyarsa tana buƙatar kuɗin domin siyan kaya saboda tafiyar da za ta yi ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ban Yi Nadama Ba: Mutumin Da Ya Taka Daga Gombe Zuwa Abuja Domin Buhari Ya Ce Zai Maimaita Idan Ya Samu Dama

Matashi ya rasa N400k a caca
Matashin na bukatar taimako domin mayar mata da kudin Hoto: Damircudic, Twitter/@tomiwa 201
Asali: Getty Images

Tomiwa ya sha alwashin dai na yin caca idan har ya samu tallafi.

Lokacin da Legit.ng ta samu tattaunawa da shi, Tomiwa ya koka kan cewa niyyar sa itace ya ninka kuɗin domin ya biya wasu ƴan buƙatun sa da kuma karatun sa na makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ina son na ninka kuɗin ne domin ina buƙatar wasu ƴan kuɗaɗe saboda buƙatu na da karatun makaranta na."

Mutane sun tofa albarkacin bakin su, kan wannan tsaka mai wuya da matashin ya tsinci kansa a ciki.

Ga kaɗan daga ciki:

@rhukieee ta rubuta:

"A matsayin ki na mace, ba za ki taɓa gane Allah tarfawa ayar ki zaƙi ba, idan mijin ki baya yin harkokin caca."

@finegirl.joy ta rubuta:

"Ko mutanen da ke da wuraren cacar nan, suna shawartar ku, da ku yi caca cikin lura, garin ya za ka kwashi har N400,000 ka sanya a caca, maimakon ka riƙa yin na 5k-5k, kamata ya yi a kama ka a hukunta ka, saboda yin caca ba bisa lura ba."

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Tsohon Dan Dambe Ya Tuna Baya, Ya Mangare Matarsa a Kan 'Remote' Din TV

Wani Matashi Ya Ɗora Bidiyon Mahaifinsu Na Musu Rabon Gado

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya nuna sha tara ta arziƙin da.mahaifin su ya yi musu da shi da ƴan'uwansa.

A cikin bidiyo, matashin ya nuna yadda mahifinsu ya gwamgwaje su da rabon gado.

Asali: Legit.ng

Online view pixel