Matashi ya Arce, Ya Bar Budurwarsa da Kawayenta 3 a Gusto Bayan Sun ci Abincin Sama da N200k

Matashi ya Arce, Ya Bar Budurwarsa da Kawayenta 3 a Gusto Bayan Sun ci Abincin Sama da N200k

  • Matashin Bakano ya bada labarin yadda budurwarsa ta kwashi kawayenta 3 suka nemi firgita tattalin arzikinsa ta hanyar cin abincin N220,00 a Gusto
  • Matashin mai suna Abdul ya bayyana cewa, abincin dubu takwas kacal ya nema amma a karon farko sun bukaci abincin N155,000
  • Zatonsa haka za a tsaya, sun zage tare da bukatar a kwai musu abincin Turai da na gida Najeriya har suka kai N220,000 wanda hakan ya rikita shi
  • Yace zai dauko katin bankinsa a mota inda daga fitarsa ya samu kira daga gida kuma yayi amfani da damar ya cika bujensa da iska

Kano - Wani matashi ma’abocin amfani da Twitter mai amfani da @iPrinceAbdul, ya za yana yadda ya arce ya bar budurwarsa da kawayenta uku a wurin cin abinci mai suna Gusto da ke Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan CBN Ya Magantu Kan Yuwuwar Tsawaita Wa'adin Amfani da Tsoffin Naira

Matashin Najeriya
Matashi ya Arce, Ya Bar Budurwarsa da Kawayenta 3 a Gusto Bayan Sun ci Abincin Sama da N200k. Hoto daga @iPrinceAbdul
Asali: Twitter

Matashin ya sanar da yadda suka jima suna hira da budurwar kafin ta bukaci ya fitar da ita kamar yadda ake wa ‘yan matan zamani.

A cewar Abdul:

”Na bata zabi, Patoosh, Gusto, Pizza Hut ko Dominos. Da kanta ta zabi Gusto da kanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

”Na je kofar gidansu amma tace in dakata Besty na fitowa. Nace wacece Besty, tace Siyama ce. Zatona wani abu ta shiga daukowa amma daga fitowarta ta shige baya ta kake.”

Matashin ya nada labarin yadda budurwarsa tace su biya Janbulo don dauko Nadiya da Ummita wadanda and su ma wasu kawayenta ne wadanda zasu fita tare.

“Daga isar mu tace a bata jerin abincin da akwai kuma da na ketare za ta fara. Ta zabi abincin da take so inda ni kuma na zabi na dubu takwas kacal.

Kara karanta wannan

Zargin Darektan Yakin Zaben Bola Tinubu a 2023, Ya Jefa Shi a Hannun Dakarun DSS

”A karon farko dai sun ci abincin sama da N155,000. A zatona shikenan, sun kara bukatar wasu abincin da suka hada da ma waje tare da na gida.
”Daga bisani an kawo min jimillar kudinmu ya kai sama da N220,000 wanda Tace a miko min. Nace zan dauko katina a mota inda daga fita ta aka kira ni daga gida ana nemana kuma na arce.”

- Abdul ya labarta.

Talauci: Matashi yace coci ta dawo masa da kudinsa

A wani labari ba daban, wani matashi ‘dan Najeriyaya bukaci cocin Dunamis da ta dawo masa da dukkan sadakarsa.

Yace keburan Talauci sun saka shi a gaba kuma yana kirga da nawa ya basu don haka su bashi kayan shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel