Yanzu-Yanzu Gwamnan CBN Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Kara Wa'adin Tsoffin Naira

Yanzu-Yanzu Gwamnan CBN Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Kara Wa'adin Tsoffin Naira

  • Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babu gudu babu ja da baya a wa'adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin kudi
  • Emefiele ya ce za a fara kama yan POS da ke chajin kudi fiye da N200 yayin cire kudi a wajensu
  • Ya ce lallai idan aka aiwatar da wannan manufar yadda ya kamata, hauhawan farashin kayayyaki zai sauka da kaso 4

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa babu bukatar dage wa’adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin kudi.

Mun dai ji cewa kotun koli ta yake hukuncin wucin gadi inda ta dakatar da gwamnatin tarayya da CBN daga aiwatar da wa’adin na daina amfani da tsoffin Naira.

Godwin Emefiele
Yanzu-Yanzu Gwamnan CBN Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Kara Wa'adin Tsoffin Naira Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Sai dai kuma, Emefiele yayin ziyarar da ya kai ma’aikatar harkokin waje don tattauna manufar kudin kasar, ya ce dage wa’adin bai da amfani, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Sai Kin Biyani N10m Zan Sake Ki: Wani Ango a Kano Ya Bukaci Sabuwar Amarya Mai Neman Saki

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Lamarin ya fara daidaita tun bayan da aka fara biyan kudi a kan kanta don kari a kan cire kudi ta ATM.
“Saboda haka, babu bukatar duba yiwuwar dage wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.”

Gwamnan babban bankin ya kuma bayyana cewa za a kama masu POS da ke chajin fiye da N200 wajen cire kudi kuma za a kai su gidan yari idan aka kama su.

Daily Trust ta kuma nakalto Emefiele yana cewa:

“Wasu daga cikin shugabanninmu suna siyan sabbin kudi suna boyewa saboda wasu dalilai kuka ni ba za zurfafa kan wannan batun ba.”

Manufar CBN zai rage yawan hauhawan farashin kayayyaki, Emefiele

Har ila yau, gwamnan CBN din ya ce babban bankin kasar na sane da mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki, yana mai cewa aiwatar da manufar na iya zabtare kaso 4 na adadin hauhawan farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Tsoho mara lafiya ya tattaro gadonsa ya dawo banki, an ki bashi kudi

Ya kuma yi bayanin cewa yawan kudaden da ke zagawa yanzu haka ya kai kimanin naira biliyan 700.

Tsoho ya sha kuka bayan ya gaza cire kudinsa a banki, ya yi wa CBN ruwan tsinuwa

A wani labari na daban, wani dattijo ya shiga tasku bayan ya isa banki don cire yan kudadensa da ke akant don ya samu damar siyar magani da abinci amma hakan ya gagara saboda manufar CBN.

Hakan ya tunzura dattijon inda ya yi tofion Allah tsine ga babban bankin kasar wanda ya ce yana kokarin tura shi kushewa tun lokacinsa ba kai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel