Allah Ya Yafe Miki: Magidanci Ya Yi Wa Budurwa Martani Bayan Ta Roke Shi Ya Zama 'Sugar Daddy' Dinta

Allah Ya Yafe Miki: Magidanci Ya Yi Wa Budurwa Martani Bayan Ta Roke Shi Ya Zama 'Sugar Daddy' Dinta

  • Wata kyakyawar budurwa mai karfin hali ta tunkari wani mutumi inda ta bayyana burinta na ya zama 'sugar daddy' dinta
  • Babu kakkautawa ko bata lokaci, mutumin ya bayyana cewa yana da aure, inda ya bukaci ta sake dubawa wani wurin ba kan shi ba
  • Budurwar da babu ko wasa ke firgici a ranta, ta tsaya tsayin daka kan cewa shi din dai ta ke, har sai da ya fada mata wani abu da bata so ba

Wata tattaunawa mai bada dariya ta faru tsakanin wata matashiyar budurwa inda ta bukaci ya zama 'Sugar Daddy' dinta, ta bar jama'a baki bude.

Budurwa
Allah ya Yafe Miki: Magidanci Yayi Budurwa Martani Bayan Ta Roke shi ya Zama 'Sugar Daddy' dinta. Hoto daga TikTok/@justkingphoebe
Asali: UGC

Budurwar 'yar asalin jihar Edo mai suna Phoebe cike da kwarin guiwa ta tunkari mutumin tare da sanar da shi cewa tana son ya zama Sugar daddy dinta.

Kara karanta wannan

"Ya Yi Bulokin Dina": Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Dandana Abincinta Ya Tsere, Ta Tambayi Dalili

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da kwarin guiwarta ya bashi mamaki, ya tambayeta daga wacce jiha ta ke amma budurwar ta ki amsawa.

"Ta yaya kyakyawar budurwa kamar ki za ta bukaci wani ya zama sugar daddy din ta?"

- Ya tambaya.

Budurwa tayi masa martani da cewa bata da aikin yi kuma ta gama karatu, don haka ta ke bukata wani da zai kula da ita.

"Ubangiji ya yafe miki. Ki zo in yi miki addu'a saboda kina neman ta."

- Mutumin cike da mamaki yayi mata martani.

Ya bukaceta da ta samu wani na daban, inda yace yana da aure.

Budurwar ta jaddada cewa shi ta ke so kuma tayi watsi da batun auren da yace yana da ita.

"A saboda haka ake kira abun da sugar daddy, kai din nake so."

Mutumin cike da mamamki yace ta zo yayi mata addu'a domin tana matukar bukatar hakan.

Kara karanta wannan

Hilda Baci: Abu 6 Da Mutum Zai Amfana Da Su Bayan Kafa Tarihi A Kundin Bajinta Na Guinness

Wannan bidiyon mai bada dariya ya samu martani daban-daban a TikTok.

Kalla bidiyon a kasa:

Soshiyal midiya tayi martani

toyinabod tace:

"Kawo kan ki mu yi miki addu'a. Kina bukatar addu'a idan ba haka ba mijin wata za ki kwace."

Gdcmedia_biz yace:

"Ko da kin samu sugar daddy, akwai bukatar ki nemi kudi."

user1579431360308 yace:

"Za ta samu sugar daddy fa da gaskiya. Matan yanzu, ka ji tsoronsu, basu san zaman lafiya ba."

Bidiyon firgicin da kare ya shiga bayan ganin zaki

A wani labari na daban, wani kare ya fada tsananin firgici bayan yayi arba da zaki.

Karen da ya hangame baki ya fara haushi, ya hadiye haushinsa bayan arangama da yayi da sarkin dawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel