Mahaifiyata ta Fada Soyayyar 'Dan Yahoo: Baturiya ta Bada Labari a Bidiyo

Mahaifiyata ta Fada Soyayyar 'Dan Yahoo: Baturiya ta Bada Labari a Bidiyo

  • Wata farar fata ta je dandalin sada zumunta don bayyana wa jama'a yadda wani 'dan damfara 'dan Najeriya ya yi soyayya da mahaifiyarta gami da takaitasu
  • Budurwar ta labarta yadda mahaifiyarta ta tura ma 'dan damfarar yanar gizon makuden kudade yayin da suke tsaka da soyayyar yanar gizo
  • 'Yan Najeriya da dama da suka yi martani game da mummunan kaddarar matar sun tausaya mata yayin da wasu suka yi mamakin yadda mahaifiyarta ke da daure amma ta ke soyayya da wanda bata sani ba

Wata budurwa farar fata mai amfani da @ashleynicole_51 a TikTok, ya je yanar gizon don bayyana yadda wani dan damfarar yanar gizon a Najeriya ya takaita mahaifiyarta da danginta.

Oyinbo Lady
Mahaifiyata ta Fada Soyayyar 'Dan Yahoo: Baturiya ta Bada Labari a Bidiyo. Hoto daga TikTok/@ashleynicole_51
Asali: UGC

Yayin wallafa bidiyon a kafar, 'diyar ta labarta yadda mahaifiyarta ta tsunduma kogin soyayyar wani 'dan damfarar yanar gizo tare da tura masa bandira 20 na kudi a cikin watanni shida.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wani Mai Sahgo da Mahaukaciya ya ba jama'a Mamaki, SUn Dinga Hira kamar Tsofaffin Masoya

A cewarta, wannan lokacin rayuwar mahaifiyarta ya kashe ma ta aure, wanda har yanzu basu farfado daga hakan ba.

Budurwar ta kara da cewa, hakan ba taba zuciyar mahaifinta, wanda ita ce ta zama mai tausarsa da bashi shawarwari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bidiyon ya tattara sama da tsokaci 2,000 da jinjina sama da 26,000 daga lokacin da aka tattara rahoton.

Jama'a sun yi martani

Legit ta tattaro wasu daga cikin martanin kamar haka:

Naomi ta ce:

"'Yan damfarar yanar gizo na aiki sosai."

Rou Rou ta ce:

" Kai. 'Yan damfarar yanar gizo sun lokacinsu. Yi hakuri."

Itshibaqxx ya ce:

"'Yan Najeriya na burge ni da wannan halin dama wa ya ce ta tsunduma kogin soyayya Karuwa kawai!"

chioma ta tambaya:

"Waya aike ta soyayya da shi?"

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

oyawiriemmanuel175 ya ce:

"Ta tsunduma soyayya da wanda bata sani ba kuma tana da aure otilo ya wuce."

urantaemelda ya ce:

"Kai!! Iyawo Pablo ya yi amfani da wasu ya siya kashi kawai."

Philip Plein ya ce:

"Ayya... Kin yi sa'a tun da ba a kullesa ba ma abun dariya."

Matashi tafe da karamin janaretonsa yana alfahari ya bada mamaki

A wani labari na daban, wani matashi ya dauka karamin janaretonsa daga gida har gidan mai domin siyan fetur.

Jama'a da dama sun dinga mamakin yadda bai je da jarka ya siya ba ya kama hanya da janareton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel