Bidiyon Yadda Mahaukaciya Ta Tara jama'a a Shagon Matashi, Ta ki Tafiya ta Bar Wurin

Bidiyon Yadda Mahaukaciya Ta Tara jama'a a Shagon Matashi, Ta ki Tafiya ta Bar Wurin

  • Wani matashi da wata mata mai rangwamen hankali sun bazu a bidiyo yayin da aka gansu suna musayar kalamai
  • Masthin 'dan Najeriyan yana tsaka da gyara kaya a shagonsa yayin da mahaukaciyar ta bayyana tare da fara damunsa
  • Ta ki barinsa shagonsa kuma ta cigaba da yi masa magana tamkar suna da sanayya tun a baya, lamarin da ya ba jama'a mamaki

Wani bidiyon matashi 'dan Najeriya yana hira da mahaukaciya wacce ta bayyana shagonsa ya yadu a soshiyal midiya.

Matashin da aka bayyana sunansa da Chiboya, bai nuna tsoronsa ga mahaukaciyar ba inda cike da wasa da zolaya ya cigaba da hira da ita yayin da yake gyara kayan shagonsa.

Mahaukaciya
Bidiyon Yadda Mahaukaciya Ta Tara jama'a a Shagon Matashi, Ta ki Tafiya ta Bar Wurin. Hoto daga TikTok/@brownchima01
Asali: UGC

A wani bidiyon TikTok da ya dauka tsawon mintuna uku, mahaukaciyar ta ki barin shagonsa duk da yunkurin da ya dinga yi wurin korarta ta bara shagonsa.

Kara karanta wannan

ANgo ya Sanar da Mutuwar Amaryarsa Bayan Kwana 11 da Shan Shagalin Aurensu, Hotunan Bikinsu Sun Girgiza Zukatan Jama'a

Ta yi masa korafin yadda zai gan ta ta wuce amma ba ya kiranta da "mahaukaciya". Amsar da ya bata tayi kama da yana kare kansa kan abinda ya ke yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani lokaci, sun tsaya tamkar za su buga dambe da juna. Legit.ng ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a jihar Ribas da ke kudancin Najeriya.

Kalla bidiyon:

Soshiyal midiya tayi martani

Betsy yare:

"Ta samu masoyi a rayuwarta."

Mammifreshy tace:

"Abun nan ba na wasa bane. fada za ku yi? Suna tambayar kawunansu. Wannan abun dariya"

ayukapam1 yace:

"Tsohon saurayinta. Wannan tsohon saurayinta ne. Mu ba wawaye bane."

ivmarian06 tace:

"Wannan shi ake kira da soyayya ta gaskiya."

udeanibonaventure yace:

"Wannan alama ce ta cewa yau zai yi kasuwa, kwastomomi ba za su daina zuwa shagonshi ba. Na taya shi murna."

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

sharonxugar tace:

"Wannan gayen mutumin kirki ne kan yadda yayi mata kamar yadda zai wa duk mai hankali duk kuwa da ya sani cewa bata da hankali. Har taba ta yayi."

genevieve070 tace:

"A yau na gane maganar da ake yi na cewa mutane da yawa basu da hankali amma kadan ne ke yawo a tituna. Hatta Chiboy din bashi da hankali"

Amarya ta rasu bayan kwanaki 11 da aurenta da angonta

A wani labari na daban, wani sabon ango ya koka da yadda amaryarsa ta rasa ranta bayan kwanaki 11 da aurensu.

Ya wallafa labarin a shafiinsa na Twitter inda jama'a masu tarin yawa suka dinga yi masa ta'aziyya da fatan alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel