Tsohuwar Budurwata Tana Son in Zama Mai Jawabi a Bikin Aurenta, Shadow

Tsohuwar Budurwata Tana Son in Zama Mai Jawabi a Bikin Aurenta, Shadow

  • Wani fitaccen mai nishadantarwa a shagulgula da bukukuwan aure Derekumar Ebiaremene Claude, wanda aka fi sani da Shadow_mcfr ya bayyana yadda tsohuwar budurwarsa ta nemi ya nishadantar a bikin aurenta
  • A cewar mutumin wanda ya kammala digirinsa na farko a jami'ar Novena ta Ogume da ke jihar Delta, budurwar tayi barin kasa-kasa da shi ne da tunanin ba zai taba nasara ba a matsayinsa na mai nishadantarwa kawai
  • Sai dai, a watan Oktobar shekarar da ta gabata, ta nemi ya nishadantar gami da taya murnar bikinta a watan Disamba, ga mamakinta jama'a sun rigata shigar da bukatarsu

Derekumor Ebiaremene Claude, wanda aka fi sani da Shadow_mcfr, wanda ya goge wajen nishadantarwa a bikin ma'aurata da taya su murna ranar aurensu, ya bayyana yadda tsohuwar budurwarsa ta bukaci a watan Oktoba da ya halarci bikinta a watan Disamba, 2022 don nishadantarwa.

Shadow
Tsohuwar Budurwata Tana Son in Zama Mai Jawabi a Bikin Aurenta, Shadow. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

A cewarsa, ta matukar shan mamakin yadda ta gano cewa an riga shigar da bukatar a gaba daya karshen makon Disamba, jaridar Leadership ta rahoto.

A cewar Shadow_mcfr, yayi mamaki saboda bata yarda gogewarsa a matsayin MC ta kai haka ba yayin da suke soyayya a jami'a, wannan na daya daga cikin dalilin da yasa tayi watsi da shi saboda a ganinta ba zai ga wata nasara a gaba ba a matsayinsa na kawai mai nishadantarwa.

Shadow_mcfr ya kammala digirinsa na farko da kwali mai daraja ta biyu (second class upper) a fannin ajiyar kudi daga babbar jami'ar Novena ta Ogume dake jihar Delta a 2014.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun daga lokacin da ya kammala bautar kasarsa (NYSC) ya tsunduma kakas harkar nishadantarwa a wurin bikin murnar nasara da na aure, yayin da ya nishadantar a bukukuwa sama da 20 a fadin jihohi 20 na kasar.

Amarya ta rasu bayan kwana 11 da aurenta

A wani labari na daban, wata amarya ta amsa kiran mahaliccinta bayan kwanaki 11 da shan shagalin aurensu.

Angonta mai suna Idris Almustapha Daja ne ya wallafa hotunansu na auren a shafinsa na Twitter inda ya bayyana rasuwarta cike da alhini.

Tuni jama'a suka dinga taya shi alhini da ta'aziyya kan wannan rashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel