Abubuwa 5 Da Ya Kamata Namiji Ya Kiyayi Faɗa Wa Mace Idan Yana Son 'Zaman Lafiya'

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Namiji Ya Kiyayi Faɗa Wa Mace Idan Yana Son 'Zaman Lafiya'

Idan aka mana tambaya, abu ne mai wahala sanin yadda mace yar Najeriya za ta yi martani idan an mata magana, tamkar lissafi mai wahalar warwarewa.

Hakan yasa yake da muhimmanci a matsayin ka namiji ka yi taka tsantsan a lokacin da ka ke hira da mace.

Duk da cewa ba wani bincike aka yi a hukumance ba, akwai wasu ka'idoji da ya kamata a kiyayye idan ana magana da mace.

Mace da Miji
Abubuwa 5 Da Ya Kamata Namiji Ya Kiyayi Fada Wa Ma Idan Yana Son Zaman Lafiya. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga tambayoyi biyar da bai kamata namiji ya rika yi wa mata ba, rahoton Premium Times.

1. "Yaushe za ki yi aure?"

Yan uwa maza, ba huruminka bane ka tambayi takwararka ko abokiyar aikina lokacin da za ta yi aure.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Mata na samun matsin lamba sosai daga al'umma da iyayensu da dangi kan aure, yi musu wannan tambayar na kara jefa su cikin damuwa.

Idan ya zama dole ka yi tambayar, ka tabbatar ka yi cikin yanayin da ya dace na mutuntaka da raha.

2. "Kina kara kiba."

Yin tsokaci kan kibar mace batu ne da ya kamata ka kame bakinka daga furtawa don muna zamani wanda ake danganta kyau da yanayin jikin mace.

Don haka, fada wa mace cewa ta yi kiba 'tamkar fada mata cewa bata cikin wadanda ake yi wa kallon suna da kyau' ne. Hakan na iya shafar kimarta a matsayin mace, ta rika ganin tamkar bata cika 'ya mace ba.

Don haka, duk yadda mace ta ke, ko mai kiba, ko siririya, ka guje yin magana kan jikinta. A yi wani hiran daban.

Idan kuma ita ta taso da batun, ka san yadda za ka yi dabara ka isar da sakonka cikin hikima.

Kara karanta wannan

“Iyayena Sun Nemi Na Bar Masu Gidansu”: Matashiya Ta Koka Bayan Tsohon Saurayinta Ya Dankara Mata Ciki

3. "Shekarun ki nawa?"

Idan dai kai ba likita bane ko jami'in yin rajista, ka guji yi wa mace wannan tambayar, musamman idan haduwarku ta farko ne.

Mata da dama ba su son a san shekarunsu, don haka yin wannan tambayar bai cika yi musu dadi ba.

4. "Ba ki da hankali."

Babu wanda ke son a kira shi mara hankali, don haka ka guji kiran matarka ko budurwa ko abikayar aiki mara hankali musamman kokacin da aka samu sabani.

Idan abu ya shiga tsakanin ka da mace kuma ka na ganin 'tana kambama abin fiye da kima' ka daure ka kwantar da zuciyarka kada ka fada mata bakar magana, don wasu na da riko a zuci sosai.

5. "Kina da juna biyu ne?."

Ina rokon ka a matsayin saurayi dan Najeriya ka guji yin wannan tambayar da mata, idan ba matar ka bane. Tambaya ce wanda ba ta yi wa mata dadi kuma ba hurumin ka bane.

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

Bidiyon Budurwa Tana Sharbar Kuka Saboda Saurayin Da Suka Fara Soyayya Tun Karamar Sakandare Ya Rabu Da Ita

Duk lokacin da mutane suka yi da ce da masu kaunarsu, ba su son wani abu da zai janyo matsala ko rabuwa tsakaninsu.

Amma dai wasu lokutan, wasu dalilai na janyo rabuwa tsakanin masoya ko da kuwa sun dade suna soyayyar.

Wata budurwa yar Najeriya ta shiga yanayi mara dadi bayan saurayin da ta fara soyayya da shi tun tana karamin aji na sakandare ya rabu da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164