Bidiyon Budurwa Tana Sharbar Kuka Saboda Saurayin Da Suka Fara Soyayya Tun Karamar Sakandare Ya Rabu Da Ita

Bidiyon Budurwa Tana Sharbar Kuka Saboda Saurayin Da Suka Fara Soyayya Tun Karamar Sakandare Ya Rabu Da Ita

  • Wata budurwa yar Najeriya ta fitar da bidiyo tana sharbar kuka saboda rabuwa da saurayinta da suka fara soyayya tun ajin karamar sakandare na 3
  • Budurwar wacce bata fayyace ainihin dalilin da yasa suka rabu da masoyin nata ba ta ce bata taba tsammanin hakan zai faru da ita ba
  • Cikin hawaye da juyayi, ta nemi mutane su taimaka mata da shawarwari kan yadda za ta iya jure wannan abin mai sosa zuciya ta kuma cigaba da rayuwarta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Duk lokacin da mutane suka yi da ce da masu kaunarsu, ba su son wani abu da zai janyo matsala ko rabuwa tsakaninsu.

Amma dai wasu lokutan, wasu dalilai na janyo rabuwa tsakanin masoya ko da kuwa sun dade suna soyayyar.

Buduwar da ta rabu da saurayinta
Bidiyon Budurwa Tana Sharbar Kuka Saboda Saurayin Suke Soyayya Tun Karamar Sakandare Ya Rabu Da Ita. Hoto: @lailasnews.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Daga siriri zuwa lukuti: Bidiyo da hotunan yadda kwarewa a girkin budurwa ya canza saurayi

Wata budurwa yar Najeriya ta shiga yanayi mara dadi bayan saurayin da ta fara soyayya da shi tun tana karamin aji na sakandare ya rabu da ita.

Budurwar ta fashe da kuma kuma ta gaza dena zubar da hawaye a wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta.

A cewar budurwar, sun fara soyayya tun lokacin suna karamar ajin sakandare na 3 (JSS3) kuma ba ta taba tsammanin za su taba rabuwa ba.

Sai dai budurwar ba ta bayyana dalilin da yasa suka rabu ba.

Ta rika kuka tana neman taimako da shawara kan yadda za ta iya jurewa ta danne zuciyarta ta cigaba da rayuwarta.

"Soyayyar da aka fara tun karamar sakandare na JSS3, yanzu daga ina zan fara," in ji ta.

Ga bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel