Attajiri Ɗan Arewa Ya Auri Matar Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Bidiyon Shagalin Bikin Ya Kayyatar

Attajiri Ɗan Arewa Ya Auri Matar Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Bidiyon Shagalin Bikin Ya Kayyatar

  • Tsohuwar matar Sillivan Chime, Clara ta samu nasarar sace zuciyar wani bayan kwashe shekaru 8 da rabuwar aurensu da dan siyasar
  • An samu bayanai akan yadda ta auri wani attajirin dan arewa wanda kirista ne inda suka yi kasaitaccen shagalin bikinsu a Jihar Abia
  • Bidiyon yadda aka yi bikin ya yadu a kafafen sada zumunta inda aka ga amaryar ta dau kyau, nan da nan ‘yan Najeriya suka fara yi mata sambarka

Abia - Tsohuwar matar tsohon gwamnan Jihar Enugu, Sullivan Chime, Clara ta kara aure bayan shekaru 8 da labarin rabuwar aurensu da dan siyasar ya yadu wanda aka zargi ya cutar da ita.

An samu bidiyon shagalin auren nata a kafafen sada zumunta wanda aka ga yadda aka gudanar da aurenta da sabon mijin nata dan arewa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Attajiri Ɗan Arewa Ya Auri Tsohuwar Matar Gwamnan Enugu, Bidiyon Shagalin Bikin Ya Kayyatar
Attajiri Ɗan Arewa Ya Auri Tsohuwar Matar Gwamnan Enugu. Hoto: @ijeomadaisy
Asali: Twitter

An yi bikin Clara da hamshakin dan kasuwar ne a ranar 29 ga watan Afirilu, a Amuda Isuochi, cikin karamar hukumar Umunnoechi da ke Jihar Abia.

An samu bayanai akan yadda sabon angon Clara din ya kasance kirista dan asalin Jihar Kaduna.

Rahotanni sun nuna yadda ta hadu da angon nata ta yaran tsohon shugaban kasan Najeriya, Umaru Yar’adua, wacce su ka yi makaranta tare.

Clara ta yi aure ne bayan shekaru 8 da rabuwarsu da Sullivan wanda aka samu rahoton cutar da ita da ya yi.

Ga bidiyon auren:

Yan Najeriya sun yi ta mata sambarka

Ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani sun dinga yi mata fatan alheri bayan samun nasarar sace zuciyar wani bayan rabuwarta da dan siyasar.

Kara karanta wannan

Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida

Legit.ng ta tsinto wasu daga cikin tsokacin:

Ugodiya_eke ta ce:

“Saukin halinta ne ya ke birge ni da ita, ina mata fatan zaman lafiya.”

Viva_drips ta ce:

“Kyakkyawar mace ce, amma ta ga rikici a aurenta na farko! Wanda ya ke gidan yari ma ya fi ta kwanciyar hankali. Amma dai yayarta ce ta ja mata. Ta gode wa Ubangijin da ya raya ta.”

Nekkyville ta ce:

“Kyakkyawa ce!!! Muna fatan Ubangiji ya dawwamar da ita cikin farin ciki.”

Maroonsmiles ta ce:

“Ta wahala sosai a rayuwa don haka ta cancanci duk wani farin ciki.”

Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter

A wani rahoton, wasu masoya, Ameenu da Yetunde, sun bayyana wa mutane yadda su ka hadu har soyayyar su ta kai su ga aure a kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda Ameenu ya wallafa wani hoto bisa ruwayar Legit.ng, inda ya nuna yadda hirar su ta kasance bayan lokacin da ya tura wa Yetunde sako a 2018.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa

Ameenu ya bayyana yadda ya fara ne da gabatar wa da Yetunde kan sa bayan ya tambayi yadda take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel