Tsohuwar matar Adam A Zango ta dawo Kannywood bayan shekaru 13
- Bayan shekaru 13, tsohuwar matar jarumi Adam A Zango ta dawo masana'anta Kannywood domin cigaba da fina-finai
- Amina Uba Hassan, ta fara fitowa a fina-finai ne a 2000, kuma ta auri Jarumi Zango a shekarar 2007 inda ta haifa masa da daya kafin su rabu
- A cewar ta, ta tuntubi mutane da dama kafin ta dauki wannan matakin na dawowa domin ta lura yin fim shine abin da ta ke kauna a rayuwarta
Kano - Amina Uba Hassan, tsohuwar matar fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango, ta dawo cigaba da yin fina-finai a masana'antar, Daily Trust ta rahoto.
Amina, wacce aka fi sani da Mamman Haidar, ta fara fitowa a fina-finan Kanywood ne a farkon shekarun 2000 amma ta auri Zango a shekarar 2007.
Ta haifi jariri na miji a shekarar 2008 amma auren su ya mutu bayan watanni biyar kamar yadda ya zo a rahoton na Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan mutuwar auren, jarumar ta dauki lokaci ba a ji motsin ta ba, sai kwatsam da fito a shirin dirama mai dogon zango na 'Gidan Danja' wacce 2Effects ta shirya.
Jaruman wacce aka haifa a garin Kaduna ta ce ta dawo Industry da karfinta a yanzu, tana mai cewa a yanzu babu gudu babu ja da baya.
Ta ce:
"Yana da wahala sosai a matsayin ta na wacce ta haihu kuma bazawara ta sake komawa industry bayan barinsa na fiye da shekaru 10, sai da na tuntubi mutane da dama tare da juriya kafin na yanke shawarar. Babu shakka, yin fina-finai shine abin da na ke kaunar yi don haka zan cigaba da yi."
Masoya da magoya baya sun yi ta yaba mata bisa yadda ta ke fitowa a shrin da ake nuna wa a Arewa24.
Adam Zango ya bayyana abu ɗaya da ya ke jira ya samu kafin ya dena yin fim kwata-kwata
A wani labarin, Jarumin Kannyood, Adam Zango ya ce akwai yiwuwar ya dena yin fim a masana'antar fim na Hausa idan ya samu wata sabuwar hanyar samun kudaden shiga, Premium Times ta ruwaito.
Jarumin ya ce a sha'awar da ya ke yi wa masana'antar na fim ta ragu duk da cewa har yanzu yana cikinta. Ya ce idan ya samu hanyar samun kudaden shiga da ta fi fim, zai dena yin fim.
A cikin hirar da aka yi da shi a BBC Hausa a ranar Asabar, Zango ya ce:
"Ni fitaccen jarumi ne a Kannywood kuma ina yi wa Allah godiya bisa wannan baiwar, amma duk da haka ina da shirin neman wata hanyar samun kudi da ta fi wannan, zan dena fim din inyi wani abu daban da zarar na samu."
Asali: Legit.ng