Tambayoyin da na baku ni ma ba zan iya amsa su ba: Abin mamaki daga lakcara a Najeriya

Tambayoyin da na baku ni ma ba zan iya amsa su ba: Abin mamaki daga lakcara a Najeriya

  • Kalaman sharhi da wani malamin Najeriya ya yi wa dalibansa a jarrabawar jami'a ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta
  • Malamin Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto ya shiga jerin ababen raha a shafukan sada zumunta na Najeriya
  • Yayin da wasu suka ji dadi da ganin sharhin malamin, wasu na ganin ba bukatar irin wannan sharhi haka

Sokoto - Da yake shiga jerin ababen raha da ke yawo a sararin intanet a Najeriya, wani malami ya ba masu amfani da shafukan sada zumunta mamaki.

An hango wasu kalaman sharhin da yayi wa dalibansa a kasan takardar jarrabawar jami’ar Usmanu Danfodio, Sokoto.

Malamin jami'a ya gigita dalibansa da tambayoyi
Tambayoyin da na baku ni ma ba zan iya amsa su ba: Abin mamaki daga lakcara a Najeriya | Hoto: @insta9jablog
Asali: UGC

Sharhin malamin

Instablog9ja ta yada kwafin takardar jarrabawar ne ta Instagram.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

A kasan takardar jarrabawar wacce ta fito daga sashin injiniyan lantarki da kayan wuta, bayanin malamin ya bayyana cewa:

"Tambayoyin da ba zan iya amsa su ba, su na tsara. Fatan nasara!"

Bayanin da ya rubuta a cikin Pidgin yana nuna cewa malamin ya yanke shawarar yin wa dalibansa tambayoyin jarrabawar da shi a matsayinsa na malami ba zai iya amsa su ba.

Legit.ng ba ta iya tantance tsawon lokacin da aka gudanar da jarrabawar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sharhin jama'a a kafar sada zumunta

@emperor_fusty001 ya ce:

“Idan wannan tambaya ce ta jarrabawar daliban 200level Electric Electronics Engineering, to Malamin mutumin kirki ne, Malamin da ma ya ba su zane, sun yi sa’a ba kawai jefo tambaya yayi ba, yace su zana da kansu kafin su yi lissafi.
"Saboda idan ba ka samu zanen daidai ba to a can matsalar take farawa wannan maganar zata baka haske, irin mutumin da yake kenan koda ace baka gane tambayar ba."

Kara karanta wannan

Mai yankan kauna: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook

@iam_davechuks ya ce:

"Ya kamata a canza sunan kasar nan zuwa Cruise Nation maimakon Najeriya. Wannan Lecturer dai haka."

@harryy_matts ne ya rubuta

"Tsarin labari: Tambayar ba za ta zama mai wahala ga daliban da suka san ainihin abin da suke yi a wannan ajin ba, ina ganin ba wani abu ne mai wahala ko kadan ba kawai wani lokacin kuna bukatar irin wannan taimako na ban dariya koda kuwa batun na da wahala, matakin damuwar ku zai sauko kuma abubuwa zasu kara girma, dalibai suna son lecturers irin wannan tbh."

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

A waje kuma, John Abraham Godson shi ne shaidar labarin cewa 'yan Najeriya za su iya jagoranci kuma su yi fice a duk kasar da suka tsinci kansu a ciki a duniya.

John wanda ya kafa tarihi a matsayin sanata bakar fata na farko a Poland za a iya yanke cewa kwararre ne idan aka yi la’akari da gogewarsa da nasarorin da ya samu.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

Dan Najeriyan wanda ya zama dan kasar Poland a 2001 kwanan nan ya nuna daya daga cikin muhimman abubuwan da yake sha'awa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.