An buɗe wa masu aikin Umrah 20,000 Masallacin Harami a yau Lahadi

An buɗe wa masu aikin Umrah 20,000 Masallacin Harami a yau Lahadi

- Mahukunta a kasa mai tsarki sun bude wa maniyata aikin Umrah su 20,000 Masallacin Harami a yau Lahadi, 1 ga watan Nuwamba

- An kuma ba masallata 60,000 damar shiga babban Masallacin don gudanar da ibadah

- Wannan shine karon farko da aka bar mutane masu yawa shiga Harami tun bayan bullar annobar korona

Rahotanni sun kawo cewa a yau Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, an bude wa maniyata aikin Umrah su 20,000 Masallacin Harami

Har ila yau an kuma ba masallata 60,000 damar shiga babban Masallacin na kasa mai tsarki domin su gudanar da ibada kamar yadda shafin Haramain Sharifain ya wallafa a Twitter.

A birnin Madinah kuma, mun ji cewa Jumullar mutum 19,500 ne za a bari domin kai ziyara ga kabarin Annabi Muhammad (SAW) daga yau Lahadi, kamar yadda Dakta Amr Al-Maddah, mataimakin ministan Aikin Hajji da Umrah ya bayyana.

Har ila yau shafin ya wallafa wasu hotuna da ke nuna maniyata cikin harami inda suka bayar da yar tazara a tsakaninsu suna addu'o'i yayin da suka fuskancin Ka'aba.

KU KARANTA KUMA: Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi

An buɗe wa masu aikin Umrah 20,000 Masallacin Harami a yau Lahadi
An buɗe wa masu aikin Umrah 20,000 Masallacin Harami a yau Lahadi Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Wannan shine karo na farko da aka bar baki daga kasashen duniya gudanar da aikin Umrah tun bayan saka dokar kulle ta annobar korona.

Adadin yau Lahadi shi ne adadi mafi yawa da za a bari su shiga Masallacin na Harami tun bayan bullar cutar korona.

Ko a lokacin Hajjin bana, adadin mutanen da aka bari suka gudanar da Aikin Hajjin ba su wuce 10,000 ba.

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan takarar shugaban kasa, Olapade Agoro, ya rasu

A wani labarin kuma, babban limamin Masallaci kasa mai tsarki, Sheikh Abdul Rahman Sudais, ya yi Allah-wadai da wadanda suka yi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Sheikh Sudais, wanda ya kasance ministan Masallatai na kasar Saudiyya a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, ya nuna rashin jin dadi tare da yin kakkausar lafazi a kan masu aibata Annabi.

Shehin Malamin ya bayyana masu irin wannan danyen aiki a matsayin kaskantattun mutane marasa daraja da kima.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel