Babbar nasara: Yan sanda sun damke gagararrun ƴan fashi, sun kwace makamai da kuɗi

Babbar nasara: Yan sanda sun damke gagararrun ƴan fashi, sun kwace makamai da kuɗi

Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutum biyu masu suna Chukwuemeka Ikechukwu, 22, da Tochukwu Okeke, 30 duk mazauna yankin karamar hukumar Idemili ta arewa da ke jihar Anambra bisa zargin aika ta fashi da makami, jaridar HumanAngle ta ruwaito.

An tattaro cewa wadanda ake zargin suna daga cikin kungiyar yan fashin da suka kware wajen yi wa jama’a fashin kayayyakinsu ta hanyar batda kammani a matsayin masu motar haya a yankunan Ogidi/Nkpor/Tarzan da Umunya, hukumar yan sandar ta bayyana.

KU KARANTA KUMA: Kalli hotuna da bidiyon tsadaddun kayayyakin Dino Melaye a gidansa da ke Abuja

Wannan tsarin fashi ana masu lakabi da ‘one chance’. Kungiyar sun shahara wajen yi wa mutane fashin wayoyi, jakunkunan hannu da sauran abubuwa marasa nauyi.

SP Haruna Mohammed, kakakin yan sandan Anambra, ya ce an samu makamai biyu, wayoyi 12 da kudi naira N290,000 wanda masu laifin suka sato yayin fashi da bindiga.

Mohammed ya ce kamun nasu a safiyar ranar 6 ga watan Satumba ya biyo bayan wani rahoton kwararru.

Babbar nasara: Yan sanda sun damke gagararrun ƴan fashi, sun kwace makamai da kuɗi
Babbar nasara: Yan sanda sun damke gagararrun ƴan fashi, sun kwace makamai da kuɗi Hoto: HumanAngle
Source: UGC

“Wadanda ake zargin sun kasance daga cikin tawagar da ke yi wa mutane fashi da makami da kwace-kwacen waya a yankunan Ogidi, Nkpor, Tarzan, Umunya, Odomodu, tollgate da kewayensu.

“Kayayyakin da aka samo daga wajensu sun hada bindiga, takoni, jakunkunan hannu biyu, wayoyi 12, karamar jaka da ke dauke da katunan waya da kuma wata adaidaita sahu.

“Sauran kayayyakin sun hada da kudi N296,000, duk wadanda suka yi kwacensu daga mutane daban-daban,” in ji shi.

Mohammed ya ce ana kan bincike cikin lamarin wanda daga bisani za a hukunta masu laifin.

KU KARANTA KUMA: Wani sojan Najeriya ya wallafa hotunan abokan aikinsa da Boko Haram suka kashe a Maiduguri

Ya yi kira ga jama’a wadanda aka yi wa kwacen wayoyi da sauran kayayyaki da su zo ofishin yan sanda na Ogbunike ko rundunar SARS da ke Akwuzu.

Ya ce wadanda ke da shedu su gabatar da su domin taimakawa binciken yan sanda. Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba ‘yan sanda hadin kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel