Rundunar 'yan sanda tayi gargadi a kan rufe lambar mota da amfani da gilashi mai duhu

Rundunar 'yan sanda tayi gargadi a kan rufe lambar mota da amfani da gilashi mai duhu

- 'Yan sanda sun gargadi masu ababen hawa a kan rufe lamba mota da amfani da gilashi masu duhu da kuma amfani da jiniya

- Rundunar ta ce wasu motoccin gwamnati ne kawai aka amince suyi amfani da jiniya ko kuma gilashi mai duhu da kuma lambobin 'yan sandan sirri

- Rundunar 'yan sandan ta bawa masu karya wadannan dokokin mako guda su cire su daga ababen hawansu domin kaucewa fushin hukuma

Rundunar 'yan sanda tayi gargadi a kan rufe lambar mota da amfani da gilashi mai duhu

Rundunar 'yan sanda tayi gargadi a kan rufe lambar mota da amfani da gilashi mai duhu
Source: UGC

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Jihar Imo ta ce ta lura akwai mutane da dama da ke rufe lambobin motarsu, amfani da gilashi mai duhu, jiniyar 'yan sanda da kuma amfani da lambobin 'yan sanda na sirri a motocci da ba na gwamnati ba.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun halaka direba a hanyar Birnin Gwari

Rundunar ta ce ba za ta ragawa duk wanda aka samu yana saba dokar hana amfani da wadandan abubuwan a motoccin da ba na gwamnati ba.

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar 'yan sanda SP Orlando Ikeokwu ya fitar a jiya, rundunar ta nuna damuwar ta a kan kallubalen da karya wadannan dokokin zai iya haifarwa a jihar musamman a lokacin da ake fuskantar zabe.

Rundunar 'yan sandan ta gargadi mutane da ke da motocci da sauran ababen da ke karya dokokin da aka lissafa su gaggauta cire abubuwan cikin mako guda domin kaucewa fuskantar fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel