El Rufa'i Ya Nemi Babbar Alkali Najeriya Ta Sauya Mai Kula Da Shari'arsa, Ya Bayyana Dalili
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya rubuta takarda ga Alkaliyar Najeriya inda ya bayyana rashin gamsuwa da yadda ake shari'arsa
- Gwamnatin Najeriya na shari'a da Nasir El-Rufa'i bisa zarge-zargen almundahana, karkatar da kudin jama'a da halasta kudin haram a wata kotun Kaduna
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana da babban korafi a kan alkalin da ke sauraron shari'ar tare da rokon Kudirat Kekere-Ekun ta kawo masa agaji
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai ƙorafi ga babbar Alƙaliyar Najeriya (CJN), Kudirat Kekere-Ekun, yana neman a sauya Alkalin da ke jagorantar shari’ar da ake masa. A cikin takardar da ya rubuta a ranar 9 ga Afrilu, 2026, El-Rufai ya buƙaci a cire R. M. Aikawa daga shari’ar, tare da miƙa ta ga wani Alƙali a sashen kotun Kaduna ko kuma wani wuri daban.

Kara karanta wannan
Dalilin gwamnan Borno na goyon bayan harin sojin sama duk da rasa rayuka akalla 200

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa El-Rufai ya bayyana cewa ci gaba da barin Mai Shari'a Aikawa ya ci gaba da shari’ar ba ya da tushe a doka da kuma ƙa’idojin aikin shari’a.
Nasir El-Rufa'i ya koka kaan shari'arsa
Daily Post ta ruwaito cewa El-Rufa'i ya ce akwai zargin nuna son kai a kansa, da kuma wasu ƙorafe-ƙorafe da ake yi wa Alƙalin waɗanda har yanzu ba a kammala bincikensu ba.
Ya ƙara da cewa Alƙalin ya ƙi janye kansa daga shari’ar duk da waɗannan matsaloli, lamarin da ya sa ya ɗauki matakin kai ƙorafi ga babbar Alkali.
Alƙali Aikawa ne ke jagorantar shari’ar tuhume-tuhume guda 10 da hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta ICPC ta shigar a kan El-Rufai da wani wanda ake tuhuma tare da shi.

Source: Facebook
Ana zargin su da laifuffuka da suka haɗa da cin amanar ofis, halasta kuɗin haram da kuma damfara da suka kai Naira miliyan 579.6 da Dala miliyan 1.1. An kuma sanya ranar 14 ga Afrilu, 2026 domin sauraron bukatar beli a wannan shari’a.
Zargin da ake yi wa El-Rufa'i
A cikin ƙorafin, El-Rufai ya ce akwai wasu ƙorafe-ƙorafe da dama da ake yi wa Alƙalin kan nuna son kai, waɗanda ke gaban babban Alƙalin kotun Tarayya da kuma hukumar shari'a.
Ya bayyana cewa shari’ar yanzu da kuma wasu shari’o’in baya suna da alaƙa da juna, wanda hakan ke haifar da abin da ya kira “bayyanannen yiwuwar son kai.
A cewarsa, ko da Alƙalin ya musanta nuna son kai, bayyanar hakan a fili kaɗai ya isa ya kawo matsala a doka.
Ya gargadi cewa barin Alƙalin ya ci gaba da shari’ar na iya lalata amincewar jama’a da bangaren shari’a, tare da jawo shakku kan gaskiya da ingancin hukuncin da za a yanke.
An dage shari'ar El-Rufa'i a kotu
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na ci gaba da jimamin rasuwar mahaifiyarsa wacce ta riga mu gidan gaskiya a cikin watan Maris na shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Za a jika wa APC aiki, tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu a Zamfara ya koma ADC
Ana cikin zaman makokin Hajiya Umma El-Rufai, tsohon gwamnan ya bayyana a gaban kotu domin ci gaba da shari'a kan tuhume-tuhumen da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ke yi masa.
Hakazalika, El-Rufai zai ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaki da rashawa ta ICPC har zuwa lokacin da kotu za ta yi hukunci kan bukatar neman belin da ya gabatar a gabanta
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
