An Lissafa Jihohin Arewa 7 da za Su Fuskanci Karancin Wutar Lantarki

An Lissafa Jihohin Arewa 7 da za Su Fuskanci Karancin Wutar Lantarki

  • Masu ruwa da tsaki a harkokin rarraba wuta sun sanar da cewa wasu jihohi bakwai a Arewacin Najeriya za su fuskanci karancin lantarki
  • Rahotanni sun nuna cewa za a samu karancin wutar lantarki a jihohin ne sakamakon wani gyara da za a yi na sama da wata daya
  • Hukumomi sun bayyana cewa wutar lantarki za ta ingana idan kammala aikin yayin da suka yi bayani kan samun wuta a lokacin gyaran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Hukumomin rarraba wutar lantarki sun sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta yi wani muhimmin gyara game da wutar lantarki.

Rahotanni sun nuna cewa gyaran zai shafi yadda ake rarraba wutar lantarki a jihohin Arewa bakwai, musamman daga safiya zuwa rana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta jero jihohi 10 da za a yi ambaliyar ruwa

Wasu ma'aitan TCN a Najeriya
Ma'aikatan kamfanin TCN a bakin aiki. Hoto: TCN Nigeria
Source: Facebook

Jihohi 7 da za a rage samun wuta

Kamfanin rarraba wuta na JED ya sanar da al'umma da ke wasu jihohin Arewa da za su samu sauyi a kan yadda suke samun lantarki a wani sako da ya wallafa a a Facebook.

Jihohin da abin zai shafa sun hada da Plateau, Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Taraba da Yobe galibinsu a Arewa masu Gabashin Najeriya.

Lokutan da za a rasa wutar lantarki

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce za a fara dauke wuta daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 22 ga Mayu, 2026, inda za a rika yi duk mako daga ranar Alhamis zuwa Lahadi tsakanin karfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin sabunta tsarin tushen wuta na kasa ta hanyar sanya wata wayar sadarwa a kan layin Jos–Gombe.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sheka ruwan sama a Kaduna, Taraba da wasu jihohi a ranar Laraba

Sanarwar ta ce:

“Hukumar tana sanar da abokan huldarta a jihohin da abin ya shafa cewa za a na katse wuta a layin Jos–Gombe daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 22 ga Mayu, 2026, wanda zai rika faruwa daga Alhamis zuwa Lahadi tsakanin karfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Ma'aikatan wutar lantarki a Najeriya.
Ma'aikatan wutar lantarki na hira da 'yan jarida a Najeriya. Hoto: TCN Nigeria
Source: Twitter

Duk da cewa an bayar da tabbacin samar da wasu hanyoyin wutar lantarki, hukumar ta gargadi masu amfani da wuta a jihohin da abin ya shafa da su yi tsammanin raguwar wuta a lokacin da ake gyaran.

A cewar hukumar:

“A lokacin katsewar, za a rika samar da wuta ta wasu layukan 132kV da ake da su."

Wutar lantarki za ta inganta a jihohin

Punch ta wallafa cewa ana sa ran za a inganta wutar lantarki a yankin ta hanyar saurin gano matsaloli, ingantaccen sarrafa wuta bayan kammala gyaran.

Hukumar ta ce amfanin da ake sa ran samu sun hada da ingantacciyar wuta, saurin dawo da wuta bayan dauke ta, karfafa tushen wuta na kasa da sauransu.

Kara karanta wannan

Raina Musulunci: An zargi Trump da kira sunan Allah a yanayi maras kyau

Legit ta tattauna da Asma'u

A tattaunawa da wata mata a jihar Gombe, Asma'u Abdul da ke unguwar Nasarawo, ta shaida cewa matsalar wutar za ta iya shafan harkokinsu na cikin gida.

"Lallai muna amfani da wuta waje dafa abinci, aiki a shagon gyaran gashi, hakan zai iya zama mana matsala saboda da rana muke aiki.
"Kasancewar man fetur ya kara kudi sosai, idan za mu yi aiki da shi ba lallai mu ci riba ba."

Rashin wuta ya karu a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu ya sanar da cewa akwai matsalar wutar lantarki a kasar nan.

Ya bayyana cewa yakin Iran da Amurka/Isra'ila na cikin abubuwan da suka haddasa matsalar wutar lantarki a fadin kasar nan a kwanan nan.

Sai dai duk da haka, Bayo Adelabu ya sanar da 'yan Najeriya cewa suna matukar kokari wajen shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng