Rikicin Jos: Malamin Musulunci Ya Fadi Yadda Ake Kulla wa Musulmi Makirci a Plateau

Rikicin Jos: Malamin Musulunci Ya Fadi Yadda Ake Kulla wa Musulmi Makirci a Plateau

  • Wani malamin Musulunci ya koka kan zargin karya da ake jingina wa Musulmi a rikicin da ke faruwa a Plateau
  • Ya ce Musulmi ma suna fuskantar hare-hare da kashe-kashe ba tare da samun adalci ba kamar yadda aka yi a baya
  • Malamin ya bukaci gwamnati ta bincika rikice-rikice tare da hukunta duk masu laifi ba tare da nuna bambanci ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani malamin Musulunci, Imam Tajuddeen Muhammad Adigun, ya yi kakkausar suka kan abin ke faruwa a jihar Plateau.

Malamin ya koka kan yada labarin karya da ke nuna Musulmi a matsayin masu haddasa rikici a jihar Plateau.

Malamin Musulunci ya kausasa harshe kan rikicin jihar Plateau
Gwamna Caleb Muftwang da Sheikh Tajuddeen Muhammad Adigun. Hoto: Caleb Muftwang, SACON MEDIA CONCEPT.
Source: Facebook

Malami ya koka kan zargin Musulmi a Plateau

Yayin da yake jawabi a masallacin MCC da ke Wuse Zone 3 a Abuja, malamin ya ce abin takaici ne yadda ake yawan dora laifi kan Musulmi duk lokacin da rikici ya barke a jihar, cewar Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Barazanar da Trump ya sake yi wa kasar Iran, ya fadi barnar da ya yi mata a yaki

Ya ce irin wannan zargi na nuna son rai da kuma rashin daidaito wajen iko, yana mai cewa Musulmi ba su da iko a Plateau da zai ba su damar shirya irin wadannan hare-hare.

A cewarsa, shugabannin jihar yawanci Kiristoci ne, kuma ba Musulmi ke rike da muhimman mukaman da za su ba su iko ba, don haka ba daidai ba ne a jingina musu dukkan laifuffuka.

Malamin ya jaddada cewa Musulunci ba ya goyon bayan kashe-kashe ko zalunci, yana mai cewa addinin ya haramta kisan bayin Allah marasa laifi.

Ya kara da cewa Musulmi da dama a jihar sun sha fama da hare-hare da kisan gilla, amma ba a ba su kulawa ko adalci yadda ya kamata.

Ya bayar da misalin kisan wani tsohon janar, Alkali, inda ya ce an gano gawarsa a wani tafki tare da gawar wasu Musulmi da dama, amma har yanzu babu cikakken hukunci kan lamarin.

Shehin malami ya caccaki yadda ake daurawa Musulmi laifi a rikicin Plateau
Taswirar jihar Plateau da ake yawan samun rikicin addini. Hoto: Legit.
Source: Original

Bukatar malamin ga gwamnatin tarayya, Plateau

Malamin ya tambayi dalilin da ya sa ba a hukunta masu laifi ba, yana mai cewa dole ne a tabbatar da adalci ga kowa ba tare da bambanci ba.

Kara karanta wannan

Rasuwar jigon APC na Kano ta tada hankali, an ji yadda ya rasu a otal a Abuja

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jihohi su dauki matakin gaggawa wajen bincike da hukunta masu aikata laifi, tare da tabbatar da zaman lafiya a kasa baki daya.

A karshe, ya yi addu’ar zaman lafiya, adalci da hadin kai a Najeriya, yana mai kira ga hukumomi su yi aiki cikin gaskiya da adalci.

An kama sojan bogi a rikicin Plateau

Mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sandan jihar Plateau ta yi karin haske kan matakan da ta ke dauka kan sabon rikicin da ya barke bayan wani hari da aka kai.

Kakakin 'yan sandan jihar, Alfred Alabo ya sanar da cewa jami'an rundunar sun kama wani sojan bogi yayin wani samame da suka kai.

An yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, su ba jami'an tsaro hadin kai yayin da hukumomi ke kokarin dawo da zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.