Abu Ya Girma: Na Kusa da Gwamna Dauda Lawal Ya Sha da Ƙyar a Harin Ƴan Bindiga
- Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan ayarin motocin makusancin Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara
- Maharan sun farmaki shugaban ma’aikatan gwamnan Zamfara, Mouktar Lugga, a hanyar Funtua zuwa Gusau da yammacin jiya Alhamis
- Lamarin ya faru kusa da ƙauyen Kucheri yayin da Lugga ke dawowa daga wani aiki, inda maharan suka fito daga bangarori biyu suka buɗe wuta kan motarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Funtua, Zamfara - Wasu ‘yan bindiga ne sun buɗe wuta kan ayarin motocin shugaban ma’aikatan gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun farmaki Alhaji Mouktar Lugga, a hanyar Funtua zuwa Gusau ranar Alhamis 2 ga watan Maris, 2026 da yamma.

Source: Original
Rahoton Zagazola Makama ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 6:16 na yamma a jiya Alhamis 2 ga watan Afrilun 2026 kusa da ƙauyen Kucheri.
Yan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara
Wannan hari na zuwa ne bayan wasu yan bindiga sun farmaki al'umma a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya da ake fama da hare-haren ta'addanci a kasar.
Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani kazamin harin ta'addanci a jihar Zamfara wacce ke fama da hare-haren yan ta'adda da ma yankin Arewa gaba daya.
Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a harin da suka kai a karamar hukumar jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana irin barnar da 'yan bindigan suka yi.

Source: Twitter
Yadda yan bindiga suka farmaki Lugga a Zamfara
Hakan na zuwa ne yayin da Lugga ke komawa Gusau bayan kammala wani aikin gwamnati a wani wuri kafin daga bisani ya hadu da iftila'in.
Majiyoyi sun ce maharan sun fito daga bangarorin hanya guda biyu, inda suka fara harbe-harbe kan motar da ke ɗauke da shugaban ma’aikatan, direbansa da wasu mutum biyu.
Rahotanni sun nuna cewa harsashi ya huda gilashin gaban motar kusa da direba, yayin da wani maharin ya kusan harbinsa amma bindigarsa ta ƙi tashi, kamar yadda rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
Duk da wannan hari, direban ya samu nasarar kauce wa wurin cikin gaggawa, inda ya tsere da motar, kuma dukkan waɗanda ke ciki sun tsira lafiya ba tare da rauni ba.
'Yan bindiga sun kashe mutane 50 a Zamfara
A baya, mun ba ku labarin cewa 'yan bindiga sun babbake kusan dukkanin gidajen garin Dutsin Dan Ajiya dake jihar Zamfara tare da kashe akalla mutane 50.
Shugaban karamar hukumar Anka, wanda ya tabbatar da harin, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun toshe kofofin tsira ga jama'a wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi da ba za su misaltu ba.
An kawo rahoton cewa mazauna garin sun yi ta maza, sun fafata da yan bindigar har na tsawon sa'o'i uku kafin harsashin su ya kare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

