Dangote, NNPCL da Gwamnoni Za Su Tara wa Uwargidan Tinubu Naira Biliyan 30
- Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya yi alkawarin bayar da tallafin abinci na Naira biliyan N20 na tsawon shekaru biyar domin tallafa wa yara
- Kamfanin mai na kasa (NNPCL) shi ma ya bi sahu da gudunmawar Naira biliyan N10 domin tabbatar da nasarar shirin raba abinci na kasa
- Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu, ta kaddamar da hukumar amintattu ta shirin "National Community Food Bank" a yau Alhamis a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja – Manyan attajiran Najeriya da kamfanoni masu zaman kansu tare da gwamnatin tarayya sun haɗa hannu a yau Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026, domin ƙaddamar da babban shirin yaƙi da yunwa da rashin tsaron abinci a faɗin ƙasar nan.
Wannan gagarumin yunƙuri, wanda uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ke jagoranta, ya samu alkawuran kuɗi da kayayyaki da suka haura Naira biliyan 30.5 a lokacin ƙaddamar da shirin.

Source: Twitter
Alkawarin N20bn daga gidauniyar Dangote
Babban attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hanyar gidauniyarsa ta Aliko Dangote Foundation, ya sanar da bayar da tallafin kayan abinci masu gina jiki na darajar Naira biliyan N20, in ji rahoton The Nation.
Shugabar gidauniyar, Zouera Youssoufou, ita ce ta sanar da wannan tallafi inda ta bayyana cewa za a raba kayayyakin ne a cikin tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Ta jaddada cewa wannan shirin zai fi mayar da hankali ne wajen ceto rayukan yara ƴan ƙasa da shekaru shida waɗanda ke fuskantar matsalar tamowa da yunwa a sassan ƙasar nan.
Youssoufou ta yi kira ga sauran rukunin ƴan kasuwa da su fito su ba da tasu gudunmawar domin ganin an kawar da yunwa baki ɗaya.
Alkawari daga kamfanin NNPCL
Shi ma kamfanin man fetur na ƙasa, wato NNPCL, bai yi ƙasa a gwiwa ba inda ya sanar da ware Naira biliyan N10 domin tallafa wa shirin a cikin shekaru biyar.
Sofia Mbakwe, wadda ta shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, ta bayyana cewa wannan yunƙuri na uwargidan shugaban ƙasa ya nuna jagoranci na gari da kishin ƙasa.
Ta tabbatar da cewa NNPC za ta yi aiki kusa da kusa da Bankin Noma (Bank of Agriculture) domin ganin tallafin ya isa ga mutanen da suka dace, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
Tinubu zai ziyarci jihohi 4, zai fara da Jos inda aka kashe Musulmai da Kiristoci

Source: Twitter
Karin tallafi daga gidaunar Emeka Offor
Baya ga waɗannan manyan kamfanoni, gidauniyar Sir Emeka Offor Foundation ita ma ta ba da tata gudunmawar ta Naira miliyan N500 domin ƙarfafa guiwar shirin.
Masu lura da al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa wannan haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƴan kasuwa zai taimaka ƙwarai wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Sanata Oluremi Tinubu ta nuna jin daɗinta kan tallafin da shirin ya samu yayin da ta rantsar da mambobin hukumar amintattu waɗanda za su kula da yadda za a gudanar da raba abincin cikin gaskiya da adalci.
'Yan Najeriya sun tarawa Remi N20bn
A wani labari, mun ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta tabbatar da cewa, 'yan Najeriya sun hada mata kudin da ya kai N20bn zuwa yanzu.
Idan ba a manta ba, Sanata Oluremi Tinubu ta nemi 'yan Najeriya su sanya kudi a gidauniyar iliminta maimakon a ba ta kyaututtukan murnar haihuwarta.
Yayin da take martani ga masu sukar manufarta, uwargidan Tinubu ta ce za ta yi amfani da kudin don karasa gina dakin karatu na kasa, wanda zai taimakai manyan gobe.
Asali: Legit.ng
