Matakai 2 da Tinubu Ya Dauka da aka Kashe Musulmai da Kiristoci a Jos
- Gwamnatin tarayya ta bayyana takaici game da salon rikicin da jihar Filato da ya salwantar da rayukan jama'a da dama
- Akalla mutane 28 sun mutu a harin Angwan Rukuba da aka yi a karshen mako, wanda ya daga hankulan yan Najeriya
- An kakaba dokar hana fita na sa’o’i 48 a Jos ta Arewa yayin da aka baza jami'an tsaro domin kawo karshen matsalar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa harin da aka kai a yankin Angwan Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato abin takaici ne.
Sai dai ta nace a kan cewa duk da tashin hankalin da rasa rayuka da aka samu, hakan ba ya nufin tsaron ƙasa ya tabarbare.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa akalla mutane 28 ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, 2026 wanda ya tayar da hankalin al’umma a jihar da ma kasa baki daya.
Gwamnati ta yi magana a kan harin Jos
Jaridar Punch ta ruwaito cewa da ya ke jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 31 ga watan Maris, 2926, Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce jami’an tsaro sun fara bin sawun wadanda suka kai harin domin kamo su.
Ministan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu da kuma al’ummar jihar Filato, yana mai cewa gwamnati tana tare da su a wannan lokaci ne na tashin hankali.
Ya bayyana cewa wannan sakon ya fito ne a madadin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma gwamnatin tarayya baki daya.
A cewarsa, jami’an tsaro sun dauki matakin gaggawa bayan samun kiran neman dauki daga yankin da abin ya faru.
Ya bayyana cewa sojoji karkashin rundunar Operation Enduring Peace sun isa wurin cikin sauri.
Jami’an tsaro sun killace yankin, sun rufe manyan hanyoyin shiga da fita, sannan suka fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata laifin.
Ya kara da cewa wadannan matakai sun taimaka wajen dakile yaduwar rikicin tare da hana aukuwar karin hare-hare.
Jos: Gwamnati na son dawo da zaman lafiya
Ministan ya bayyana cewa wannan mataki wani bangare ne na tsarin tsaro da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a jihar Filato da yankin Arewa ta Tsakiya baki daya.
Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro da suka hada da sintiri da kuma amfani da bayanan sirri domin gano masu laifi a yankunan da ke cikin hadari.
Haka kuma, an kara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake fargabar hare-hare, tare da hadin gwiwar sojoji da ‘yan sanda domin karfafa tsaro.

Source: Twitter
Ministan ya bayyana cewa shugaban kasa ya gudanar da wani taro na musamman da manyan hafsoshin tsaro domin duba halin da ake ciki da kuma daukar sababbin matakai.
Ya kuma ce an gayyaci Gwamnan jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang, domin tattaunawa kan yadda za a samar da dawwamammen zaman lafiya.
Bayan harin, an kakaba dokar hana fita na sa’o’i 48 a Jos ta Arewa domin tabbatar da tsaro da bai wa jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
An kama sojin bogi a Jos
A baya, mun wallafa cewa rundunar 'yan sandan jihar Filato ta yi karin haske kan matakan da ta ke dauka kan sabon rikicin da ya barke bayan wani hari da aka kai.
Kakakin 'yan sandan jihar, Alfred Alabo ya sanar da cewa jami'an rundunar sun kama wani sojan bogi yayin wani samame da suka kai yankin da mummunan lamarin ya faru.
An yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, su ba jami'an tsaro hadin kai yayin da hukumomi ke kokarin dawo da zaman lafiya a yankin Rukuba da Filato baki daya
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


