Bayan Karuwar Hare Hare, Najeriya Ta Fadi Aikin da Sojojin Amurka ke yi a Kasar
- Rundunar tsaron Najeriya ta yi kira ga dakarunta da su kara sanya ido sosai yayin da ake shirin bikin Easter a ranar Litinin, 6 ga Afrilun 2026
- Kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ya yi bayani game da irin tallafin da sojojin Amurka ke bayarwa duk da karin hare-hare
- Sojojin Amurka sama da 100 sun zo Najeriya ne tun a lokacin da aka fara maganar zargin kashe Kiristoci a karshe-karshen shekarar 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta sanya sojoji cikin shiri a faɗin ƙasar nan gabanin bikin Easter, tare da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an ƙara tsaurara matakai.
DHQ ta kuma sake jaddada cewa tallafin da ake samu daga Amurka na ƙara ƙarfafa yaƙi da ta’addanci, inda ake sa ran za a fara ganin tasirinsa cikin makonni masu zuwa.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ya tabbatar wa jama’a cewa sojoji na cikin shiri yayin bikin Easter a Najeriya.
Shirin sojoji kan bikin Easter
Onoja ya ce rundunar soji ta riga ta sanya jami’anta cikin shirin ko-ta-kwana a duk faɗin ƙasar domin hana duk wata barazana ta tsaro a lokacin hutun.
Ya ƙara da cewa an dauki irin waɗannan matakai a lokutan bukukuwa da suka gabata kamar Kirsimeti da Sallah, kuma za a ci gaba da hakan.
“Mun san cewa lokacin bukukuwa yakan zo da ƙarin barazanar tsaro. Rundunar soji ta ba da umarni domin dukkan jami’ai su kasance cikin shiri. Wannan karon ma ba zai bambanta ba,”
Inji shi
Batun sojojin Amurka a Najeriya
Dangane da haɗin gwiwa da sojojin Amurka, Onoja ya ce watakila ba za a ga tasirin nan take ba saboda yanayin ayyukan soja, amma ya nuna ƙwarin gwiwa cewa sakamakon zai bayyana a cikin makonni da watanni masu zuwa.
Ya ce tallafin Amurka yana da matuƙar muhimmanci musamman a bangaren musayar bayanan sirri da horaswa, yana mai cewa ana bayar da taimakon domin ƙarfafa yaƙi da ta'addanci.
The Nation ta wallafa cewa ya ce:
“Kun san suna ba mu bayanan sirri da horaswa, wanda mu ke buƙata. Su na ba mu wannan cikin sharudda da aka yi. Akwai abubuwa da dama da ba zan iya faɗa ba saboda sirri ne.”

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa bayanan sirrin da ake bayarwa sun haɗa da gano wuraren da barazana da masu tayar da hankali suke, yana mai cewa sojojin Najeriya za su ɗauki matakin da ya dace.
An kashe Musulmai a Filato
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta sanar da cewa an kashe Musulmai 4 a wani hari da aka kai unguwar Rukuba a jihar Filato.
Kungiyar ta ce bayan kashe wasu, akalla Musulmai 10 ne da ba a san a ina suke ba har yanzu tun ranar Lahadi da aka kai harin.
Rundunar 'yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewa an kashe akalla mutum 27 a harin, yayin da wasu ke kwance a asibiti suna jinya.
Asali: Legit.ng

