An Sako Isra'ila a Gaba a Najeriya, Malamai na So Tinubu Ya Raba Hanya da Netanyahu

An Sako Isra'ila a Gaba a Najeriya, Malamai na So Tinubu Ya Raba Hanya da Netanyahu

  • Wata kungiyar Musulunci a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yanke alaka da kasar Isra'ila saboda yakin da ake da Iran
  • Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar, AbdulRazzaq AbdulWahab Al-Amin Aladodo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar
  • A bayanin da ya yi, Sheikh AbdulRazzaq AbdulWahab Al-Amin Aladodo ya kawo dalilai da ya ce ya kamata su sanya yanke alaka da Isra'ila

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata ƙungiyar Musulunci, Al-Harakatul Islamiyyah, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yanke hulɗar diflomasiyya da Isra’ila tare da yin tir da Amurka a fili kan rikicin da ke gudana da ya shafi Iran.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa ci gaba da zama a kan katanga na nufin goyon bayan abin da ta kira “zalunci” a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Pakistan ta gana da Iran, an taɓo batun sulhu da Amurka

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na sauraron jawabi a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa Al-Harakatul Islamiyyah ta yi wannan kira ne a ranar Juma’a yayin bikin Ranar Qudus da ta shirya domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa da kuma jawo hankali kan ƙarin tashin hankali a yankin.

Neman Najeriya ta rabu da Isra'ila

A cikin wata sanarwa da shugabanta, AbdulRazzaq AbdulWahab Al-Amin Aladodo, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta buƙaci Najeriya ta daina zama a kan katanga, ta ɗauki matsaya mai ƙarfi kan yakin Iran.

Daily Trust ta rahoto sanarwar ta ce:

“Kiran dakatar da faɗa kawai ba tare da ɗaukar mataki ba tamkar wasa ne, domin an san waɗanda ke haddasa rikicin,”

Inda ta zargi Isra’ila da Amurka da haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin.

Ƙungiyar ta buƙaci Najeriya ta yanke hulɗa da Isra’ila, tana mai nuni da take hakkin bil’adama da ake zargin ana yi a Gaza da kuma takunkumin da aka sanya kan Masallacin Kudus.

Kara karanta wannan

Mayakan Houthi sun shigawa Iran yaki, sun yi ruwan wuta a Isra'ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu na bayani a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Magana kan Gaza da Falasdinawa

Kungiyar ta ambaci rikicin da ke gudana a Gaza da sauran tashin hankali a yankin a matsayin hujjar matsayarta, tana mai cewa ci gaba da hulɗa da Isra’ila na rage ƙoƙarin tabbatar da adalci a duniya.

Al-Harakatul Islamiyyah ta danganta rikicin da ya shafi Iran da gwagwarmayar Falasɗinawa, tana mai cewa rawar da Tehran ke takawa na da muhimmanci wajen yaƙi da Isra’ila.

Ƙungiyar ta ce abubuwan da ke faruwa yanzu na nuna ci gaba da rikice-rikicen siyasa da suka daɗe suna faruwa dangane da batun Falasɗinu, inda ta nuna cewa rikici a yankin ya ƙaru.

Kira ga kasashen Musulmi na duniya

Ƙungiyar ta kuma buƙaci ƙasashen Musulmi, musamman karkashin GCC, su sake duba alaƙarsu da ƙasashen waje tare da cire sansanonin sojojin ƙasashen waje daga yankunansu.

Ƙungiyar ta ƙara kira ga haɗin kan ƙasashen Musulmi, tana mai gargadin cewa rarrabuwar kawuna na ci gaba da raunana martanin haɗin gwiwa kan matsalar Falasɗinu.

Kara karanta wannan

Yaki zai fadada: Kasar Afrika 1 tilo ta fito za ta taya Isra'ila yakar Iran

“Dole ne al’ummar Musulmi su haɗa kai su kuma yi amfani da duk wata hanya wajen goyon bayan Falasɗinawa,”

Inji sanarwar.

Trump ya ce man Iran ya ke so

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya fito ƙarara ya nuna cewa yana son amfani da man fetur din kasar Iran.

Trump ya bayyana haka ne wata daya bayan kaddamar da yaki a kasar Iran, duk da bai taba fitowa fili ya nuna yana son man fetur din kasar ba.

Yayin da ya ke samun matsin lamba kan cigaba da yaki da Iran, Trump ya ce wawaye ne ke caccakar shi kan kokarin kwace man Iran da karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng