NiMet: Za a Yi Ruwan Sama a Kaduna, Yobe, Wasu Jihohin Arewa a Yau Talata
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa jihohin Arewa za su fuskanci zafi da rana tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama da yamma
- A bisa hasashen hukumar a jihohin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran samun ruwan sama tun da sanyin safiya sannan a samu rana daga baya
- A Kudu kuwa, NiMet ta ce za su fuskanci ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa cunkoso da jinkirin zirga-zirga abubuwan hawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Talata 31 ga Maris, 2026, inda ta bayyana yiwuwar sauyin yanayi a sassa daban-daban na ƙasar nan.
A cewar rahoton hukumar, za a samu yanayi mai zafi da rana a yankin Arewa, yayin da ake sa ran tsawa da ruwan sama su biyo baya a wasu wurare daga rana zuwa yamma.

Source: Facebook
A sakon da NiMet ta wallafa a Facebook, ta ce za a yi gajimare da ruwan sama a jihohin Arewa ta Tsakiya da Kudancin kasar nan.
Jihohin Arewa da za a yi ruwan sama
A Arewa, hukumar NiMet ta bayyana cewa za a fara da samun rana mai ƙarfi a yawancin jihohi, musamman da zarar gari ya waye.
Sai dai a wasu wurare a jihohi kamar Taraba, Adamawa, Borno, Yobe da Kaduna, ana iya samun tsawa tare da ruwan sama matsakaici tun daga safiya.
Daga rana zuwa yamma kuwa, hasashen NiMet ya nuna cewa tsawa da ruwan sama za su ƙaru a jihohi irin su Taraba, Bauchi, Yobe, Gombe, Kaduna da Adamawa.
Hukumar ta jaddada cewa duk da zafin rana da ake sa ran za a fuskanta, akwai yiwuwar samun iska mai ƙarfi kafin saukar ruwan sama, don haka ta shawarci jama’a da su kula da lafiyarsu ta hanyar daukar matakan da suka dace.
Za a yi ruwa a Arewa ta Tsakiya
A Arewa ta Tsakiya da ya haɗa da Babban Birnin Tarayya Abuja, jihohin Plateau, Benue da Nasarawa, ana sa ran za a yi gajimare da kuma rana da safe.
Sai dai daga rana zuwa yamma kuwa, NiMet ta yi hasashen cewa tsawa da matsakaicin ruwan sama za su mamaye yankin gaba ɗaya.
Ruwan sama zai sauka a wasu jihohin Kudu
A jihohin Kudancin Najeriya kuwa, hasashen da hukumar NiMet ta yi ya nuna cewa za a samu gajimare tare da ɗan hasken rana da safe.
Rahoton hukumar NiMet ya bayyana cewa ihohi irin su Ondo da Edo za su iya fuskantar tsawa da ruwan sama tun da safe.
Daga rana zuwa yamma, ana sa ran ruwan sama mai yawa zai shafi jihohi da dama ciki har da Lagos, Ogun, Oyo, Ondo, Osun, Ekiti, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Abia da Imo.
Gargadin NiMet ga 'yan Najeriya
Domin kare lafiya da dukiyar 'yan kasa, hukumar NiMet ta bukaci jama’a da su kula da matakan tsaro yayin tsawa da ruwan sama a jihohi.
Hukumar ta gargadi 'yan Najeriya da su guji tsayawa a fili ko karkashin manyan itatuwa a lokacin da ake tsawa a yankunan su.
Haka kuma, NiMet ta shawarci matukan abubuwan hawa, musamman babur da su yi taka-tsantsan a hanyoyi masu santsi saboda kaucewa zamewa.

Source: Original
Bugu da ƙari, an shawarci kamfanonin jiragen sama da su rika samun cikakken bayani kan yanayin filayen jirage kafin tashi, domin kauce wa matsalolin da ka iya tasowa sakamakon sauyin yanayi.
NiMet ta yi hasashen ruwan sama
A wani labarin, mun kawo muku hasashen da hukumar NiMet ta yi game da samun ruwan sama a ranar Litinin, 30 ga Maris, 2026.
A bayanin da hukumar ta yi, NiMet ta ce za a samu ruwan sama da ke hade da iska mai karfi a jihohin Gombe, Taraba da sauransu.
Haka zalika ta bayyana cewa za a samu ruwan sama sosai a Kudancin Najeriya, inda ta bukaci jama'a su dauki matakan kariya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


