Tsaro: Hankula Sun Tashi kan Ganin Dan Amurka na Yawo a Kauyukan Najeriya
- Masana da masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun fara magana kan wani dan kasar Amurka, Alex Birbir da ke yawo a kauyukan Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa Alex Birbir na shiga kauyuka ne a jihohin Arewa ta Tsakiyan Najeriya da sunan wa'azi da wayar kan Kiristoci
- Yawon da Alex Birbir ke yi ya fara daukar hankali ne bayan ganin shi a wajen da aka kai hari aka kashe mutane da dama a cikin dare a Filato
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - 'Yan Najeriya sun fara tambayoyi game da wani dan kasar Amurka da ke yawo a kauyukan Najeriya bayan fara maganar kisan Kiristoci.
Wasu masu sharhi sun bayyana cewa akwai hadari ganin yadda Alex Birbir ke yawo a kauyaka, musamman kan alakar Musulmi da Kirista a yankunan.

Source: Twitter
Korafi kan dan Amurka a Najeriya
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama na cikin wadanda suka yi tambayoyi ga mahukunta a X kan ganin Alex Birbir na yawo a kauyuka.
Ya yi tambaya da cewa:
"Me ya sa Alex Birbir yake wajen da aka aikata laifi? Me ya faɗa wa matasa har bayan haka suka fara kashe mutane, suna kashe matafiya marasa laifi yayin da wasu suka jikkata?"
"Wa ya ba shi izinin gudanar da irin waɗannan ayyuka a yankuna masu hatsari? Me ya sa ake ganinsa da bindiga a ƙasarsa kamar soja, amma duk lokacin da ya dawo Najeriya sai ya riƙa sanya gajeren wando yana kiran kansa mishan na Kirista? Asali waye wannan mutum?"
Ya kara da cewa:
"Me ya sa hukumomi ba sa kula da ayyukansa? Jiya ma ya yi barazana ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Kalaman sa da saƙonninsa suna daɗa tayar da hankali."
Yushau Shuaib ya yi tambayoyi
Dan jarida mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Yushau Shuaib ya yi tsokaci game da yadda Alex Birbir ke yawo a kauyukan Najeriya.
Ya fitar da sanarwa a Facebook yana cewa:
"Wa ya ba wannan baƙon, Alex Barbir, damar yawo a Arewa ta Tsakiya yana gudanar da abin da ka iya haifar da tashin hankali tsakanin Kiristoci da Musulmi a Arewa? Har ma ana ganinsa yana tafiya tare da jami’an tsaro, kamar yadda hoton nan ya nuna."
Ya yi gargadi da cewa da cewa tarihi ya nuna yadda wasu jami’an leƙen asirin ƙasashen waje ke amfani da dabarun yaƙin tunani domin tarwatsa ƙasashe kamar yadda aka gani a Libya, Syria da Sudan.

Source: Twitter
Korafin Misbahu kan dan Amurka
Wani dan jarida, Misbahu El-Hamza ya ce a baya-bayan nan, an ga kiraye-kiraye daga Jasawa da ke neman gwamnati ta binciki Alex Barbir.
A sakon da ya wallafa a Facebook, ya ce:
"Abin mamaki, jiya an gan shi a wurin da aka aikata laifi a Unguwan Rukuba, Jos ta Arewa, yana ɗaukar bidiyo bayan harbe-harben da suka yi sanadin mutuwar mutane marasa laifi.
"Amma abin lura shi ne, ɗan ƙasar Amurka ne. Saboda tashin hankali na baya-bayan nan tsakanin Najeriya da Amurka, wasu ‘yan Najeriya na ganin gwamnati na iya kauce wa ɗaukar mataki a kansa.
An kai hari jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda sun kai hari a wani yanki na jihar Filato a daren Lahadi, inda suka kashe mutane da dama.
Biyo bayan lamarin, gwamnatin jihar Filato ta saka dokar hana fita na wani dan lokaci domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Jihar Filato dai na cikin jihohin Arewacin Najeriya da suke fama da matsalolin rashin tsaro, wanda suka jawo mutuwar dubban mutane a tsawon shekaru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


