Malamin Addini Ya Tuna Rayuwarsa Ta Fashin Banki a Baya, Ya Fadi Yadda Ya Shiryu

Malamin Addini Ya Tuna Rayuwarsa Ta Fashin Banki a Baya, Ya Fadi Yadda Ya Shiryu

  • Fasto Ezekiel Dachomo ya yi magana kan rayuwar da ya yi a baya wanda ke cike da laifuffuka daban-daban
  • Dachomo ya bayyana yadda ya taba zama shahararren dan ta’adda da dillalin kwayoyi a kauyensu kafin ya tuba
  • Ya ce ya shiga fashi da banki a shekarar 1980 tare da abokinsa, amma daga baya ya mika rayuwarsa ga Yesu wanda ya canza shi gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Fasto Ezekiel Dachomo ya sake bayyana rayuwarsa ta baya wanda ke cike da aikata laifuffuka.

Dachomo ya ce ya taba zama shahararren dan ta’adda da dillalin kwayoyi a kauyensu kafin Allah ya taimake shi ya tuba.

Fasto ya tuna rayuwar banza da ya yi a baya
Babban Fasto daga jihar Plateau, Ezekiel Dachomo. Hoto: Ezekiel Dachomo.
Source: Instagram

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, manyan wakilan jam'iyyar 3 sun mutu a hatsarin mota

Yadda Fasto ya shiryu daga aikata laifuffuka

Dachomo ya danganta sauyin rayuwarsa da addininsa na Kirista, yana mai cewa ya samu sabon shugabanci bayan ya tuba daga aikata laifuffuka da dama.

Malamin addinin ya bayyana haka ne yayin wani taron addini inda ya bayar da shaidarsa ta yadda ya tuba daga rayuwar da ya shafe shekaru yana yi.

Faston ya kuma yi ikirarin cewa ya shiga aikata laifuffuka daban-daban a lokacin samartakarsa, ciki har da fashi da makami.

Ya ce:

“Na kasance shahararren dan ta’adda a wannan kauye, dillalin kwayoyi a wannan kauye, mai yawo ba tare da tsari ba, wannan ce shaidata.
“Idan na ambaci shekarar 1980, mu ne muka yi fashin banki, kuma wanda ya jagoranci aikin abokina ne na kusa.”

Ya kara da cewa rayuwarsa ta sauya ne bayan ya karbi Yesu a lokacin da ya ke cikin wannan hali na aikata laifi.

A cewarsa, ya mika rayuwarsa gaba daya ga Yesu wanda yake matsayin mai ceto a gare shi, kuma hakan ya kawo masa gafara.

Kara karanta wannan

Aminu Gwarzo: "Abin da yasa na hakura da kujerar Mataimakin gwamnan Kano"

Ya ce:

“Na mika kaina ga Yesu, wanda shi ne mai ceto na, na bar shi ya jagoranci rayuwata, kuma ya gafarta mini zunubaina.”
Fasto ya fadi yadda ya shiryu bayan fashi da makami
Fasto a jihar Plateau da ke korafi kan cin zarafin Kiristoci, Ezekiel Dachomo. Hoto: Ezekiel Dachomo.
Source: Facebook

Halin da Fasto Dachomo ke ciki yanzu

Dachomo ya jaddada cewa yanzu ya zama sabon mutum a cikin addinin Kirista bayan wannan sauyi da ya samu a rayuwarsa.

Sai dai kuma, bayan wadannan kalamai, mutane da dama sun fara sukar sa tare da kira ga hukumomi su bincike shi.

Wasu na ganin cewa kamata ya yi a gurfanar da shi a gaban kuliya bisa ikirarin da ya yi na aikata ta'adi a baya.

Haka kuma, wasu sun zarge shi da kara rura wutar rikicin manoma da makiyaya da ake fama da shi a yankin.

Sun ce an ji shi yana kira ga matasa da su tashi su shiga yaki, abin da ya jawo cece-kuce a tsakanin al’umma.

Fasto ya magantu kan garkuwa da mutane

An ji cewa malamin addini a jihar Plateau ya yi magana kan masu garkuwa da mutane inda ya yi wa mabiyansa gargadi kan biyan kudin fansa.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Mataimakin gwamnan Kano, Gwarzo, ya yi murabus daga mukaminsa

Fasto Ezekiel Dachomo ya ce idan an sace shi, kada a biya fansa, yana mai cewa jininsa zai haifar da yaki na ’yantar da Kiristoci.

Malamin ya bayyana cewa ya yarda da haɗarin da yake ciki game da kisan gilla a Arewa, musamman waɗanda ke kai wa Kiristoci hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.