Zo Ku Nema: Gwamnati Ta Bude Shafin Shirin Tallafa wa Ƴan Najeriya Miliyan 10
- Gwamnatin tarayya ta fara yi wa 'yan Najeriya miliyan 10 rajistar ba su horon sana'o'i da ilimin sarrafa kudi kyauta a fadin kasa
- Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tabbatar da cewa shirin zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin 'yan kasa
- Hukumomi sun yi gargadi cewa wannan shirin kyauta ne don haka 'yan Najeriya su guji bada kudi ga kowa yayin cike fom din shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fadar shugaban kasa ta ƙaddamar da shirin yi wa ‘yan Najeriya rajista domin ba su horo kyauta a fadin ƙasar nan.
Wannan gagarumin shiri, wanda ke da nufin ilimantar da mutane miliyan 10 kan tsarin hada-hadar kuɗi da dogaro da kai, na ɗaya daga cikin manyan ayyukan raya ƙasa na Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
An fara rajistar bada horo ga matasa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da fara rajistar shirin a ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2026, in ji rahoton Daily Trust.
Shettima, wanda Mai ba shugaban kasa shawara kan tattalin arziƙi, Dr. Tope Kolade Fasua ya wakilta, ya bayyana cewa wannan shiri zai sauya rayuwar ‘yan Najeriya sannan ya zama abin koyi ga duniya baki ɗaya.
"Kaddamar da wannan shirin zai zama daga daga cikin manyan shirye-shiryen Shugaba Bola Tinubu da za su amfani 'yan Najeriya."
- Kashim Shettima.
Fannonin da za a horar da 'yan Najeriya
Kamfanin WAWUAfrica, wanda ke kan gaba wajen horar da mata a Afirka, shi ne zai tafiyar da tsarin rajistar, a cewar rahoton Channels TV.
Shirin ya ƙunshi fannoni daban-daban na ilimi da fasaha domin tabbatar da cewa kowa ya amfana. Ga wasu daga cikin fannonin da mataimakin shugaban kasar ya lissafa:
- Ilimin na’ura mai ƙwakwalwa da fasahar sadarwa.
- Ilimin hada-hadar kuɗi da tattalin arziƙi.
- Sana’o’in hannu, injiniyanci, da ƙere-ƙere.
- Kiwan lafiya, nishaɗi, da yawon buɗe ido.
- Kasuwanci da dabarun neman kuɗi.

Source: Twitter
Gargadi: 'Wannan horo kyauta ne'
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman, Dr. Nurudeen Zauro, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hattara domin kada wasu su yaudare su.
Ya jaddada cewa wannan horo kyauta ne baki ɗayansa, kuma ba a buƙatar kowa ya biya ko sisin kwabo domin shiga tsarin.
Gwamnati ta ce tana aiki kafada da kafada da bankin duniya, kungiyar AU, ECOWAS, da hukumar NITDA domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin shirin.
Gwamnati ta ce za ta ci gaba da faɗaɗa wannan shirin har sai an cimma burin da aka sa gaba na ganin kowane ɗan ƙasa ya san yadda zai sarrafa kuɗinsa.
Za a ba matasan Najeriya horo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta kawo shirin EIBIC domin ba 'yan Najeriya damar koyon sana'o'i da bunkasa tattalin arzikinsu.
Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatar ilimi ta kasa ce za ta jagoranci tsara shirin da gudanar da shi domin karfafa matasan kasar nan.
A bayanin da ta yi, ma'aikatar ilimi ta sanar da cewa a gobe Juma'a, 27 ga Maris, 2026 za a kaddamar da shirin a birnin tarayya Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

