EIBIC: Gwamnatin Najeriya Ta Kawo Shirin ba Matasa Horo da ba Su Jari
- Gwamnatin tarayya ta kawo shirin EIBIC domin ba 'yan Najeriya damar koyon sana'o'i da bunkasa tattalin arzikinsu da na kasa baki daya
- Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatar ilimi ta kasa ce za ta jagoranci tsara shirin da gudanar da shi domin karfafa matasan kasar nan
- A bayanin da ta yi, ma'aikatar ilimi ta sanar da cewa a gobe Juma'a, 27 ga Maris, 2026 za a kaddamar da shirin a birnin tarayya Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya, ta hannun ma’aikatar ilimin Najeriya, na shirin ƙaddamar da shirin EIBIC a fadin ƙasa baki daya.
An ƙirƙiri shirin ne domin bai wa matasan Najeriya ƙwarewar aiki, ilimin kasuwanci da tallafin haɓaka kasuwanci domin ƙarfafa kirkire-kirkire da ci gaban sana’o’i.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game kaddamar da shirin da yadda zai gudana ne a wani sako da Ma'aikatar ilimi ta tarayya ta wallafa a shafinta na X.
Dalilin kawo shirin EIBIC ga matasa
A bayanin da aka fitar a ranar Laraba, an bayyana cewa an tsara shirin ne domin ƙarfafa matasa ‘yan kasuwa, inganta bunƙasar sana’o’i.
Haka zalika an sanar da cewa shirin zai fito da rawar da ilimi ke takawa wajen sauya tattalin arzikin Najeriya da ci gaban ƙasa da zai shafi kowa da kowa.
Gwamnatin ta ce shirin EIBIC zai taimaka wajen cike gibin da ke tsakanin mallakar takardar shaidar karatu da kwarewar zahiri, ta hanyar bai wa mahalarta horo kai tsaye da tallafin da ake bukata domin kafa kasuwanci mai dorewa.
Karin bayani kan shirin EIBIC
Sanarwar gwamnatin ta ƙara da cewa shirin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, ƙarfafa kirkire-kirkire, da hanzarta ci gaban tattalin arziki a faɗin ƙasar.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa shirin zai sa ilimi ya zama babban ginshiƙi wajen ƙara yawan aiki da ci gaban ƙasa, ta hanyar daidaita ilimi da bukatun masana’antu.
Yaushe za a kaddamar da shirin?
Rahotanni sun nuna cewa za a ƙaddamar da shirin EIBIC a ranar Juma’a, 27 ga Maris, 2026, a dakin taro na TET Fund da ke Abuja.
Ma'aikatar ilimi ta kara da cewa ana sa ran taron zai fara da ƙarfe 9:30 na safe, yayin da mahalarta za su fara isa daga ƙarfe 9:00 na safe.

Source: Twitter
Hukumomi sun sanar da cewa masu ruwa da tsaki daga gwamnati, jami’o’i, masana’antu da ƙungiyoyi za su halarci taron.
Daga cikin abubuwan da za a gabatar akwai bayyana tsarin shirin, gabatar da manufofinsa, da kuma bude damar haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.
Rashin wuta ya shafi sana'o'i a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Ministan makamashi, Bayo Adelabu ya sanar da cewa rashin wuta da ake fama da shi a kasar nan ya shafi al'umma da dama.
A wani bayani da ya yi, ministan ya ce masu sana'o'i da 'yan kasuwa za su samu koma a baya a kan matsalar wuta da ake fuskanta a yanzu.
Adelabu ya bukaci 'yan Najeriya da su kara hakuri tare da cewa gwamnati ta dukufa wajen ganin ta shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

