An Bankado yadda Gwamnati Ta Ba 'Abokin Tinubu' Kwangilar Naira Tiriliyan 1.4

An Bankado yadda Gwamnati Ta Ba 'Abokin Tinubu' Kwangilar Naira Tiriliyan 1.4

  • Kamfanin ITB Nigeria, mallakin Gilbert Chagoury ne zai aiwatar da aikin gyaran tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tin Can a birnin Legas
  • An kiyasta cewa wannan aikin zai lakume Naira tiriliyan 1.4, kuma gwamnatin Tinubu za ta samo rancen kudin gudanar da aikin daga Birtaniya
  • Chagoury, ya kasance babban abokin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya ba shi lambar girmama ta biyu mafi girma a Najeriya, watau GCON

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa kamfanin gine-gine na ITB Nigeria ne zai aiwatar da gagarumin aikin gyaran manyan tashoshin jiragen ruwa na Legas, watau Apapa da Tin Can Island.

Shi dai kamfanin ITB Nigeria, wani reshe ne na rukunin kamfanonin hamshaƙin ɗan kasuwar nan ɗan asalin ƙasar Lebanon da ke Najeriya, Gilbert Chagoury.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock

Aminin Tinubu, Gilbert Chagoury ya samu kwangilar Naira tiriliyan 1.4
Gilbert Chagoury (na biyu daga hannun hagu) ya na jawabi a wata ganawar Shugaba Bola Tinubu da shugaban Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

Alakar Bola Tinubu da Gilbert Chagoury

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar kasuwanci tsakanin Chagoury da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ƙara fitowa fili, duba da cewa su biyun aminan juna ne na tsawon shekaru da dama, in ji rahoton Daily Trust.

A farkon wannan shekara ta 2026, Business Day ta rahoto Shugaba Tinubu ya karrama Gilbert Chagoury da lambar yabo ta biyu mafi girma a ƙasar, watau Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).

Shugaban ya bayyana cewa ya ba aminsa, Chagoury wannan lambar ne sakamakon gudunmawar da yake bayar wa a bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya.

Sai dai, masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na kallon wannan karramawa da kuma ba shi manyan kwangiloli a matsayin wani salo na nuna fifiko ga aminan shugaban ƙasa.

Yarjejeniyar kuɗaɗe tsakanin Najeriya da Birtaniya

A makon jiya ne aka ƙulla wata yarjejeniyar tallafin kuɗi har fam miliyan 746 tsakanin Najeriya da ƙasar Birtaniya yayin wata ziyarar aiki da Shugaba Tinubu ya kai birnin London.

Kara karanta wannan

29 ko 30: Malamin addini ya riga sarkin Musulmi, ya sanar da ranar karamar Sallah a Najeriya

Wannan yarjejeniya, wacce aka sanya wa hannu a gaban Firayim Minista Keir Starmer, za ta samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen farfaɗo da manyan tashoshin jiragen ruwa guda biyu na Legas domin inganta harkokin shigo da fitar da kaya.

Bincike ya nuna cewa Gilbert Chagoury yana cikin tawagar da ta biyo Shugaba Tinubu zuwa Downing Street a London, inda aka kammala tattaunawar kuɗaɗen.

A ƙarƙashin wannan yarjejeniya, hukumar bayar da lamuni ta Birtaniya (UKEF) za ta tsaya wa Najeriya wajen samun rance domin gudanar da aikin.

Darajar kwangilar da aka ba abokin Tinubu

A karshen shekarar 2025 ne ministan harkokin tattalin arzikin ruwa, Gboyega Oyetola, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta ware dalar Amurka biliyan ɗaya (N1.4tr) domin zamanantar da waɗannan tashoshi.

Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da ITB Nigeria a matsayin kamfanin da zai jagoranci aikin, wanda ake sa ran zai kawo sauyi ga yadda ake gudanar da ayyukan sufuri a Najeriya, in ji rahoton This Day.

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ce ta amince a ba kamfanin ITB Nigeria kwangilar manyan tituna.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da zai fara jagorantar taron majalisar FEC a Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Gilbert Chagoury ya kafa rukunin kamfanoninsa ne a shekarar 1971, kuma tun daga lokacin kamfanin ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanoni a Afirka.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Baya ga wannan sabon aikin na tashoshin jiragen ruwa, kamfanonin Chagoury ne ke gudanar da:

  • Hanyar Lagos zuwa Calabar: Aikin da za a kashe wa Naira tiriliyan 15.
  • Birnin Eko Atlantic: Wani katafaren birni da ake ginawa a kan teku a Legas.
  • Banana Island: Tsibirin da ya zama mazaunin manyan masu kuɗin Najeriya.

Duk da cewa kamfanonin nasa sun shahara wajen gina ayyuka masu inganci, ana ci gaba da sukar yadda gwamnatin Tinubu ke ba shi kusan dukkan manyan kwangilolin ƙasar.

Atiku ya zargi Tinubu kan kwangilar titi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da rufa-rufa wajen bayar da kwangilar babban titin Legas-Kalaba da ke Kudancin Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar titin mai tsawon kilomita 700, kuma titin zai ratsa ta cikin jihohi tara.

Atiku Abubakar ya ga baiken gwamnatin na kin bawa wasu kamfanonin damar nuna sha'awar gudanar da aikin titin, da kuma kin bayyana ainihin kudin kwangilar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com