Sheikh Mansur Sokoto Ya Yi wa Tinubu Tsirara kan Matsalolin Musulmi a Najeriya

Sheikh Mansur Sokoto Ya Yi wa Tinubu Tsirara kan Matsalolin Musulmi a Najeriya

  • Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kira ga malamai masu tallan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027 mai zuwa
  • Malamin ya bayyana cewa shugaban kasar ya ci zabe da gumin Musulmi a zaben 2023 ba tare da jama'a sun ga wani abu a kasa ba
  • Mansur Sokoto ya bukaci malamai su rika bayyana nasarorin da Tinubu ya samu da cigaban da ya kawo maimakon jingina shi da addini

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da watsi da Musulmi bayan ya yi amfani da su wajen samun nasara a zaben 2023.

Malamin ya ce tikitin Musulmi da Musulmi da Tinubu ya yi amfani da shi wata dabara ce ta siyasa domin samun mulki, yana mai cewa Musulmi da yankin Arewa ba su amfana da gwamnatinsa ba.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock

Sheikh Mansur Sokoto da Bola Tinubu
Sheikh Mansur Sokoto a hagu, Shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Prof. Mansur Sokoto, mni
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa malamin ya fadi haka ne yayin da ya ke huduba a ranar Juma'a da aka yi sallar azumi kamar yadda ya wallafa bidiyon bayanin da ya yi a shafinsa na Facebook.

Korafin Mansur Sokoto kan Bola Tinubu

Farfesa Mansur Sokoto ya nuna damuwa kan yadda al'ummar Musulmi ke shan wahala a mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A cewarsa, Tinubu ya lashe zaben 2023 ne da tikitin Musulmi da Musulmi, amma a yanzu Musulmi na cikin wahala a karkashinsa, ba ya yi wa Musulmi ko Musulunci aiki.

Ya kara da cewa yankin Arewa wanda mafi yawansa Musulmi ne ma ba shi ne a gabansa ba, ya ce abin da ya fi damunsa shi ne Lagos kawai, kuma har a Lagos din ma, abokan hulɗarsa Kiristoci ne.

Sheikh Mansur Sokoto ya ce:

"Babu shakka cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci zabe a 2023 da gumin Musulmi, amma kamar yadda kowa ke gani, Musulmi na shan wuya a karkashin wannan gwamnatin."

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya bijirewa Sarkin Musulmi, zai yi sallar azumi a yau Alhamis

Gargadi ga malamai masu tallar Tinubu

Malamin ya gargadi sauran malamai da kada su rika tallata Tinubu a zabukan gaba bisa addini, yana mai bukatar su maida hankali wajen bayyana ayyukan da ya yi idan har akwai.

A cewarsa, ya kamata ‘yan Najeriya su goyi bayan shugaban kasa ne kawai idan gwamnatinsa ta inganta ilimi, kiwon lafiya, noma, kasuwanci, tattalin arziki da kuma wutar lantarki.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce duk wanda zai yi wa Tinubu kamfen ya fadi abin da ya yi wa 'yan Najeriya, idan kuma babu to ya ce ya kamata a bari jama'a su duba wani ko za su samu mai dama-dama.

Fadar shugaban kasa ta yi shiru

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kokarin jin ta bakin fadar shugaban kasa kan wannan zargi da malamin ya yi bai yi nasara ba.

An turawa fadar shugaban kasa tambayoyi amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu amsa daga masu magana da yawun Tinubu ba.

Kara karanta wannan

'Ku yi koyi da Annabi SAW': Malami ga Sanusi II, Aminu Bayero kan hawan salla a Kano

NLC ta yi wa Tinubu korafi

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC ta yi korafi kan yadda ma'aikata ke shan wahala a Najeriya saboda matsalolin tattalin arziki.

Kungiyar da bukaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kafa kwamiti na musamman domin karawa ma'aikata albashi a Najeriya.

NLC ta kara da cewa bai kamata mafi karancin albashi ya yi kasa da N150,000 lura da yadda kudin kayayyaki suka tashi sosai a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng