Seyi Tinubu Ya Fadi Abin da Mahaifinsa Ke Yi wa Najeriya da ba a Sani ba
- Dan shugaban Najeriya, Seyi Tinubu ya bukaci matasan Najeriya su yi hakuri tare da amincewa da shugabancin mahaifinsa
- Ya ce gwamnatin na kokarin gyara matsalolin da suka dade suna damun kasar duk da halin kunci na tattalin arziki
- Seyi ya nuna goyon baya ga sake zaben mahaifinsa a 2027, yana mai cewa gyare-gyaren za su amfani al’umma a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Seyi Tinubu, ya sake ba yan Najeriya hakuri kan shugabancin mahaifinsa.
Seyi ya bukaci matasan Najeriya su kasance masu hakuri tare da amincewa da manufofin gwamnatin mahaifinsa.

Source: Twitter
A cikin wani bidiyo da ke yawo da The Nation ta bibiya, Seyi ya ce duk da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta, gyare-gyaren da ake yi za su haifar da alheri mai dorewa.
Yadda Seyi Tinubu ya dauko tafiyar matasa
Wannan na zuwa ne yayin da Seyi Tinubu ya fara gina wata tafiyar siyasa ta matasa a fadin Najeriya baki daya domin zaben shekarar 2027.
Tafiyar da aka sanya wa suna 'City Boy Movement' ta samu karbuwa a wurin wasu matasa da dama musamman a Arewacin Najeriya.
Kungiyar na ba da mukamai da dama ga matasa a matakan shugabanni na yankuna da jihohi da kuma unguwanni.
Francis Oluwatosin Shoga wanda shi ne Darekta-janar na tafiyar ya bayyana jin dadi kan taron kungiyar da aka yi a Kudu maso Gabas.
Shoga ya bayyana haka a shafin tafiyar da aka wallafa a Facebook inda ya godewa Seyi Tinubu bisa goyon baya da yake ba su.

Source: Facebook
Jan hankalin da Seyi ya yi ga matasa
Seyi ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kokarin magance matsalolin da suka dade suna damun kasar tun shekaru da dama.
A cewarsa, maimakon a bar wadannan matsaloli su ci gaba, shugaban kasar ya dauki matakin gyara su domin samar da kyakkyawar makoma.
Seyi Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya musamman matasa su ci gaba da yin addu’a ga shugaban kasar da kuma fatan sake zabensa a 2027.
Ya ce mahaifinsa na jagorantar kasar zuwa wani sabon salo da ba a taba gani ba a baya.
Haka kuma ya yabawa kokarin da shugaban ke yi wajen gina tushe mai karfi ga ci gaban kasar nan gaba.
Ya kara da cewa manufar wannan gyara ita ce samar da kasa mai ingantaccen tsari da al’umma za su amfana da ita a nan gaba.
Seyi ya jaddada cewa wannan zai taimaka wa matasa da kuma ‘ya’yansu su rayu cikin kasa mai ingantaccen tsarin rayuwa.
Tinubu ya yaba wa dansa, Seyi
Mun ba ku labarin cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rubuta sako mai ratsa zuciya ga ɗansa, Seyi Tinubu a bikin cikarsa shekaru 40 da haihuwa.
Shugaba Tinubu ya yi godiya ga Allah SWT, yayin da ya kuma lissafa wasu daga cikin halayyar Seyi na son jagoranci da ci gaban mutane.
Sannan ya kara da yi wa 'dansa addu'a, yana mai bayyana yadda ya ke alfahari da matakan da ya ke dauka wajen gina rayuwar jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

