Abin da ake Cewa kan Trump Ya Gargadi Tinubu bayan Harin Maiduguri
- A daren Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026 wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai harin kunar bakin wake Borno
- Biyo bayan lamarin, an yada wani sako a kafafen sada zumunta da aka ce shugaba Donald Trump ya gargadi Bola Tinubu kan harin
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta gudanar da bincike game da sahihancin sakon da aka ce shugaban Amurka ya tura wa Tinubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Harin kunar bakin wake da ake zargin kungiyar Boko Haram ta kai wasu wurare uku a jihar Borno ya dauki hankali a Najeriya.
An wallafa wani sako a kafafen sada zumunta da ke nuna lamarin ya dauki hankalin shugaban Amurka, Donald J. Trump, kuma ya yi gargadi ga Bola Tinubu.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin sakon da 'yan Najeriya da dama suka wallafa a kafafen sada zumunta suna cewa daga shugaba Trump ya fito zuwa ga Tinubu.
Me aka ce Trump ya fada wa Tinubu?
Sakon da mutane da dama suka yada a intanet ya yi ikirarin cewa shugaba Trump ya gargadi Tinubu game da harin da aka kai Maiduguri.
Ga abin da wani sashe na sakon ya kunsa:
“Halin da ake ciki a Najeriya babban bala’i ne. Manyan hare-haren kunar bakin wake da aka shirya sun faru a daren yau a Maiduguri. An kai hari Asibiti, babbar kasuwa, da ofishin gidan waya!
"Mutane da dama sun mutu. Wannan shi ne abin da ke faruwa idan babu shugabanci na gari!
"A yayin da kasarsa ke cikin wannan halin, shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kasar Birtaniya wata ‘ziyara’. Abin takaici!
"Ban yarda da haka ba! Ya kamata Firaminista Starmer ya gaya masa ya hau jirgi ya dawo gida nan take! Ba za ka zauna a kasashen waje ba yayin irin wannan rikici.”
Da gaske Trump ya fadi haka ga Tinubu?
Legit Hausa ta bibiyi shafukan sada zumunta na shugaba Donald Trump tare da wasu jami'an gwamnatin Amurka ba tare da ganin sakon ba.
Mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Abubakar Gambo ya wallafa a Facebook cewa:
"Na goge rubutuna na baya game da Trump bayan wasu mutane da dama, ciki har da masu amfani da kafar Truth Social, sun nuna cewa rubutun na bogi ne. Na gode.

Source: Facebook
Malamin a jami'ar kasar Jamus, Muhsin Ibrahim ya wallafa a Facebook cewa:
“Wannan rubutu da ake yadawa da sunan Trump game da fashewar bam a Maiduguri da kuma Tinubu na karya ne. Duk da cewa sakon na iya zama mai ma’ana, amma ba gaskiya ba ne.”
"Allah Ya kawo karshen wannan kashe-kashen, Ya ji kan wadanda suka rasu, kuma Ya bai wa iyalansu juriyar jure wannan rashi, amin."

Kara karanta wannan
Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri
A karshe, sakon da ake fada cewa Donald Trump ya fadawa Tinubu ba gaskiya ba ne duk da cewa har yanzu fadar shugaban kasa bata yi martani ba.
Mutum 108 sun jikkata a Maiguduri
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Borno ta fitar da rahoto game da harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri.
Kakakin 'yan sanda ya sanar da cewa an kai harin ne wurare uku da suka hada da kasuwar Monday Market da sauran wuraren da ake hada-hada.
Bayan fara bincike game da harin, 'yan sanda sun bayyana cewa mutum sama da 100 ne suka jikkata a harin tare da rasa rayuka sama da 20.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

