Marigayi Buhari, Pantami da Manyan da aka Yada Labarin Karyar za Su Yi Aure
A ƴan kwanakin nan ne aka samu labarin cewa jagoran NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na dab da angwancewa a cikin wannan na Maris, 2026 da ake ciki.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba shi ne babban dan siyasa na farko da aka rika yamaɗiɗin cewa zai kara aure ba.

Source: Facebook
A cikin ƴan shekarun nan, an samu labarai daban-daban da ke alakanta manyan ƴan siyasa da batun karin aure, sai daga baya a gano ƙarya ne.
Daga ƴan siyasa har zuwa sauran taurari da ƴan wasa, babu wanda ya tsira daga irin wadannan jita-jita. An ga lokacin da hakan ta faru da Tijjani Gandu da Maryam Booth.
Legit ta tattaro wasu daga cikin manyan ƴan siyasa a Najeriya da aka yi masu ƙaryar ƙara aure, yayin da suka fito domin ƙaryata zancen.

Kara karanta wannan
Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran
Yan siyasa da aka yiwa ƙaryar ƙara aure
Wasu daga cikin ƴan siyasa da aka ce za su kara aure alhali karya ne sun haɗa da:
1. Muhammadu Buhari da Sadiya Umar Farouq
This day ta ruwaito tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouq, ta musanta jita-jitar da ke cewa tana shirin auren tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan magana ta fara yawo.

Source: Twitter
Ministar ta ce rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana dab da yin aure da Buhari labari ne na ƙarya da bai kamata a ɗauka da muhimmanci ba.
Sadiya Farouk ta bayyana cewa ita da Buhari sun daɗe suna zumunci tun shekaru da dama, har matar tsohon shugaban ƙasar, Aisha Buhari, ma ƙawarta ce kuma kamar ‘yar’uwa take.
Ta ce:
“Don haka ina son mu ci gaba da wannan kyakkyawar dangantaka da muke da ita,” in ji ta.
2. Rabiu Musa Kwankwaso da Rabi’atu Idris Labari
A ƴan kwanakin nan ne aka samu labarin da ya karade shafukan sada zumunta cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zai ƙara auren.
Saifullahi Hassan, hadimin tsohon gwamnan ya wallafa a Facebook cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba shi da niyyar ƙara aure a lokacin da aka maganar.

Source: Facebook
Rahotanni da suka yadu a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Kano zai angwance da wata mata mai suna Hajiya Rabi’atu Idris Labari a ranar 29 ga watan Maris 2026 a jihar Katsina.
Amma Saifullahi ya ce Duk da an buga Katsina, batun ba shi da tushe balle makama, don haka ya bukaci jama’a su yi watsi da jita-jitar.
3. Aisha Buhari da Isa Ali Pantami
Kwanaki tsohon mai taimaka wa marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya yi magana game da jita-jitar auren Aisha Buhari.
Daily Post ta wallafa cewa Bashir Ahmad ya musanya rahotannin da ke cewa tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari za ta auri tsohon Ministan sadarwa Isa Ali Pantami.
Lamarin ya samo asali ne bayan wani katin gayyatar aure da aka kirkira ta bayyana a kafafen sada zumunta, inda aka yi ikirarin cewa Pantami zai auri Aisha Buhari.

Source: Facebook
Bashir Ahmad ya ce babu wani mutum mai hankali da zai ɗauki irin wannan labari da muhimmanci.
Ya ce:
"Labarin da ake yadawa cewa Hajiya Aisha Buhari ta amince za ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne tsagwaronsa, babu gaskiya ko kaɗan a ciki.”
Rahoton ya bayyana ne kasa da shekara guda bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
4. Ned Nwoko da Chika Ike
Sanata Ned Nwoko ya musanta jita-jitar da ke cewa yana shirin auren jarumar Nollywood Chika Ike a matsayin matarsa ta bakwai.
A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, an bayyana cewa rahotannin ba su da tushe kuma hasashen banza ne da wasu suka kirkira, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Source: Instagram
Jita-jitar ta fara ne bayan matarsa, Regina Daniels, ta rufe shafinta na Instagram, abin da ya jawo mutane suna hasashen akwai matsalar aure a tsakaninsu.
Sai dai ofishin sanatan mai mata da dama ya karyata duka zarge-zargen, yana mai cewa labaran ƙarya ne da wasu masu rubutun yanar gizo ke kirkira domin jan hankali.
Ofishin ya kuma bukaci jama’a su yi watsi da irin waɗannan jita-jita, su kuma dogara ne da sahihan bayanai daga hukumance.
5. Ibrahim Babangida da Ummi Ibrahim
Jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim da aka fi ni da Zeezee, ta tabbatar da jita-jitar cewa a baya tana soyayya da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da take magana kan jita-jitar da ta dade tana yawo a kafafen sada zumunta, kamar yadda PM ta ruwaito.
A wancan lokacin da aka rika jta-jitar za su yi aure, Ummu ta ce Ibrahim Babangida saurayinta ne, amma sun rabu.

Source: Twitter
Ta ce:
“Tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida saurayina ne a wancan lokaci, amma yanzu ba haka ba ne.”
Sai dai ta kara da cewa a halin yanzu suna matsayin abokai ne kawai kuma suna mutunta juna. Hakan na zuwa ne shekaru bayan rasuwar Maryam Babangida.
6. Dino Melaye da Susu
Sanata Dino Melaye na daga cikin manyan da aka rika yada labarin kanzon kuregen cewa zai yi aure, inda shi kuma ya fito ya ƙaryata zancen da kansa.

Source: Facebook
PM News ta ruwaito cewa Dino, wanda ya taba rabuwa da matarsa a baya, ya bayyana cewa labarin da ke cewa zai auri wata mata da ake kira Susu ba gaskiya ba ne. Ya kara da cewa bai taba haduwa da matar ba balle har a ce zai aure ta, inda ya nemi jama'a da jama’a su yi watsi da batun.
Ruwa ya kifar da masu zuwa aure
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta nuna alhini kan rasuwar wasu mata daga cikin masu rakiyar amarya a haɗarin jirgin ruwa a karamar hukumar Yauri.
Gwamna Nasir Idris ya nuna matukar damuwa game da rasuwar matan, haka zalika Shugaban karamar hukumar Yauri inda matan suka fito domin zuwa taya murnar aure
Wasu rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 100 ne a cikin kwale-kwalen da ya yi hadarin, inda akalla mata 13 suka riga mu gidan gaskiya yayin da aka ceto wasu
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




