Hukumar EFCC Ta Cafke Mai Martaba Sarki, Ana Zargin Ya Yi sama da Faɗi da N150m

Hukumar EFCC Ta Cafke Mai Martaba Sarki, Ana Zargin Ya Yi sama da Faɗi da N150m

  • Hukumar EFCC ta cafke sarkin Okpella, Mai Martaba Michael Sado kan zargin karkatar da Naira miliyan 250 na kudin al'ummar da yake mulka
  • Ana zargin basaraken da bude asusun banki na sirri domin kwashe kudaden diyar hakar ma'adinai da kamfanin Dangote yake biya a jihar Edo
  • Shugabannin kauyen Ukhomuniyo ne suka shigar da karar inda suka bayyana cewa basaraken ya maida kudaden jama'a tamkar na kansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Edo - Hukumar EFCC ta kama sarkin Okpella dake ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo, Mai Martaba Michael Sado (Okuokpellagbe na Okpella), tare da wani Injiniya Patrick Omkhagbo.

Kamun nasu na zuwa ne sakamakon zargin hannu a wasu ayyukan damfara da suka shafi kuɗaɗen al'umma waɗanda aka samar daga albarkatun ƙasa dake yankin.

Kara karanta wannan

Ana tunanin azumi 30, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa ga musulman Najeriya

EFCC ta kama wani basarake a Edo bayan samun korafin yana sama da fadi da kudin al'ummarsa.
Hedikwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ke Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Facebook

EFCC ta cafke mai martaba sarki a Edo

Jami'an EFCC daga shalkatar hukumar dake Benin ne suka kama basaraken bayan karɓar wani korafi daga majalisar shugabannin ƙauyen Ukhomuniyo, in ji rahoton Leadership.

Masu ƙorafin, ta hanyar lauyoyinsu na ofishin A.O. Osagie & Associates, sun zargi sarkin da mayar da yankin Ukhomuniyo tamkar mallakinsa ta hanyar karkatar da kuɗaɗen al'umma zuwa asusunsa.

A cewar takardar ƙarar, basaraken ya karya yarjejeniyar ci gaban al'umma dake tsakanin kamfanin siminti na Dangote da mutanen Ukhomuniyo.

Wannan yarjejeniya, wacce aka ɗauko daga sashe na 116 na dokar ma'adinai ta Najeriya ta shekarar 2007, ta tanadi cewa al'ummar da ake hako ma'adinai a filayensu suna da haƙƙin samun kuɗaɗen bunƙasa ƙasa duk shekara.\

Ana zargin sarki da karkatar da N250m

Masu ƙarar sun bayyana cewa yarjejeniyar ta tanadi cewa kamfanin simintin Dangote zai rika biyan kuɗi har naira miliyan 250 duk shekara ga al'ummar yankin.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

Sai dai, an zargi sarkin da buɗe wani asusun banki na daban da sunan "Okpella Community Development" ba tare da amincewar jama'a ba, sannan ya maida kansa shi kaɗai ne mai ikon sanya hannu a asusun domin kwashe kuɗaɗen.

Wannan lamari ya haifar da gagarumin tashin hankali a garin na Okpella, inda rahotanni suka nuna cewa basaraken ya yi barazanar kunna rikici tsakanin 'yan garin idan aka ci gaba da bincikar zarge-zargen dake kansa.

Ana zargin basaraken yana yin babakere kan kudin al'ummarsa da suke samu daga Dangote.
Taswirar jihar Edo da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana yi wa basarake tambayoyi a EFCC

Shugabannin al'umma sun bayyana cewa sun shafe tsawon lokaci suna roƙon matasa da su kwantar da hankulansu domin guje wa zubar da jini duk da cewa sun dade suna son daukar mataki.

Wata majiya daga ofishin EFCC dake Benin ta tabbatar da cewa kamun da aka yi wa sarkin da injiniyan wani abu ne da aka saba yi, yayin da aka karɓi irin wannan ƙorafi, in ji rahoton The Guardian.

Majiyar ta bayyana cewa sakamakon tambayoyin da ake yi wadanda ake zargin ne zai nuna mataki na gaba da hukumar za ta ɗauka.

EFCC ta gayyaci masu nadin sarki

A wani labari, mun ruwaito cewa, EFCC ta gayyaci masu zaben sarki daga masarautar Oyo don amsa tambayoyi kan zargin karɓar na goro a wajen fitar da sabon Alaafin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, ta fadi dalili

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu zaben sun karɓi rashawa mai yawa don fifita wani ɗan takara, wanda ya ja hankalin EFCC.

Hukumar ta tabbatar da cewa bincike ya kankama kuma wasu daga cikin masu naɗin sun amsa gayyatar, sauran za su bayyana cikin makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com