Isra'ila Ta Ji Ruwan Wuta, Ta Fara Karaya a Shirin da Ta Yiwa Gwamnatin Musulunci ta Iran
- Isra'ila ta nuna alamun karaya da shakku kan yunkurinta na kifar da gwamnatin Musulunci ta kasar Iran a yakin da suke yi a Gabas ta Tsakiya
- Wani babban jami'i a gwamnatin Isra'ila ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Iran ta juyin juya hali tana da goyon bayan 'yan kasar
- Wannan na zuwa ne bayan Firaminista Benjamin Netanyahu ya bukaci al'ummar Iran su fito su jagoranci gwagwarmayar sauya gwamnati
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Kasar Isra'ila ta fara karaya a yakin da take yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran duk da hadin gwiwar da ta yi da Amurka.
Rahotanni tsun nuna cewa Isra'ila karkashin jagoranci Firmaninista, Benjamin Netanyahu tak fara fargabar cewa da wuya ta iya sauya gwamnatin Musulunci ta Iran.

Source: Facebook
A rahoton da RFI ta kawo, Isra'ila ta fara nuna shakku kan yiwuwar cimma burinta na canza gwamnatin Iran duk kuwa da an kashe jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan
Masu leken asiri sun gano abin da ba zai yiwa Amurka da Isra'ila dadi ba kan kasar Iran
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke cewa sojojin ƙasarsa sun kai hari kusan ko’ina a cikin Iran, musamman a babban birnin ƙasar, Tehran.
Gwamnatin Iran na da goyon bayan jama’a
Yayin da aka shiga rana ta 13 tun bayan fara wannan yaƙi ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, wani jami’i a gwamnatin Isra’ila ya ce babu alamun gwannatin Iran za ta ci kasa.
Babban jami'in na Isra'ila ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa har yanzu gwamnatin musulunci ta Iran na da goyon bayan jama’ar ƙasar.
A cewarsa, wannan na nufin cewa zai yi matuƙar wahala a kifar da gwamnatin duk da hare-haren da ake kaiwa.
Sai dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha bayyana cewa yaƙin da ƙasarsa ke yi zai iya ba wa ‘yan Iran damar kawar da shugabanninsu su karɓi mulki.
Har yanzu ana musayar wuta da Iran
A lokaci guda, Iran na ci gaba da harba makamai masu linzami zuwa cikin Isra’ila, inda wasu hare-haren suka shafi yankuna da dama ciki har da birnin Tel Aviv.

Kara karanta wannan
Bayan kwana 10 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila ya mika bukata 1 ga mutanen Iran
Haka kuma Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Tehran, ciki har da farmakin da ya jikkata sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei.
Da yake magana kan yadda yaƙin ke gudana, Shugaba Trump ya ce sojojin Amurka sun kai hari a kusan dukkan wuraren da suka ke da muhimmanci a cikin Iran.
Sai dai ma’aikatar tsaron Amurka ta kuma ce tana duba yiwuwar kai hare-hare kan wasu tashoshin jiragen ruwa na fararen hula, inda take zargin cewa daga wuraren ne Iran ke kai wasu hare-hare.
Iran ta kara raunata mutane a Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta bayyana adadin mutanen da suka samu raunaka sakamakon hare-haren da Iran ke kai wa kasar.
Ma'aikatar lafiyar ta bayyana cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kai mutane 179 da suka ji rauni zuwa asibitoci sakamakon rikicin da ake yi da Iran.
An ruwaito cewa adadin mutanen da suka raunata sakamakon hare-haren makamai masu linzami na Iran ya haɗa da fararen hula da kuma sojoji.
Asali: Legit.ng