Nuru Khalid da Malaman da aka Dakatar daga Wa'azi kafin Alkali Zariya
A tarihin Arewacin Najeriya na baya bayan nan, gwamnatoci da kungiyoyin addinin Musulunci sun dakatar da malamai daga wa'azi saboda wasu dalilai.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A makon da ya wuce shugaban majalisar malaman Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya dakatar da Sheikh Alkali Salihu Zariya daga tafsirin Ramadan.
Hakan ya sanya Sheikh Alkali Zariya shiga cikin jerin malaman addinin Musulunci da aka taba hanawa yin wa'azi na wani lokaci a Najeriya.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo muku rahoto na musamman game da malaman da aka taba dakatarwa daga wa'azi a Arewacin Najeriya.
1. An dakatar da Sheikh Abduljabbar a Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya haramta wa Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara yin wa’azi tare da bayar da umarnin rufe masallacinsa a 2021.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100
A lokacin, Daily Trust ta rahoto Ganduje ya ce gwamnatin jihar ba za ta bari mutum guda ya haddasa rikici ko ya kawo cikas ga zaman lafiya da zaman tare cikin lumana a jihar ba.
Ya ce:
“Muna sa ido sosai kan dukkan ayyukansa. Jami’an tsaro suna lura ƙwarai da abin da yake yi, kuma kamar yadda kuka gani mun ɗauki mataki.”

Source: UGC
A yanzu haka Sheikh Abduljabbar yana rufe a gidan gyaran hali saboda hukuncin kisa da aka yanke masa bayan wata mukabala da malamai suka yi da shi.
Bayan mukalabalar, an tuhumi malamin da rashin iya kare kan shi daga zargin yi wa Annabi SAW batanci.
2. An dakatar da Nura Khalid a Abuja
A 2022 shugaban kwamitin masallacin Apo a Abuja, Sanata Muhammadu Dansadau ya dakatar da limaminsu, Sheikh Nuru Khalid saboda wani karatu mai zafi da ya yi a kan tsaro.
Bayan dakatar da shi, daga baya Sanata Muhammadu Dansadau ya bayyana cewa masallacin ya kori Sheikh Nuru Khalid saboda bai nuna nadama ba.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa malamin ya bayyana cewa gara ya rika daukar kaya ana biyansa kudi, maimakon ya daina fadin gaskiya.

Kara karanta wannan
Ganin fetur ya tashi a duniya, Tinubu ya bada umarnin gaggawa a kawo wa 'yan Najeriya sa'ida

Source: Facebook
3. An dakatar da Sheikh bin Usman a Kano
A shekarar 2025 Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a da ake kira Masjid Sahaba, ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Usman daga jagorantar sallah da gabatar da huduba, bayan wata huduba da ya gabatar.
Daily Nigerian ta rahoto cewa a cikin hudubar da ta jawo ce-ce-ku-ce, Bin Usman ya bayyana yadda aka “yi masa rashin adalci” tare da rage masa matsayi a tafiyar da harkokin masallacin.
Hudubar da ya gabatar a ranar 24 ga Janairun 2025 ta jawo fushin masu ibada, har ta kai ga kusan kai hari ga sakataren kwamitin amintattun masallacin, Abdulkadir Isawa.

Source: Facebook
Hukumar gudanarwar masallacin, a cikin wata wasika da daraktan gudanarwa ya sanya wa hannu, ta dakatar da Bin Usman ba tare da kayyade lokaci ba, amma daga baya ya koma tsohon masallacinsa.
4. An dakatar da Alkali Zariya
A watan Ramadan 1447, Shugaban Malaman Izala na kasa, Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya dakatar da Alkali Abubakar Salihu Zariya daga tafsiri a Damaturu, jihar Yobe.
Alkali Salihu Zariya ya yi wa'azi mai zafi game da rashin tsaro, inda ya kira sunayen wasu manyan shugabanni ya musu tatas kan zargin rashin daukar matakin da ya dace.

Source: Facebook
Mutane da dama sun yi kira ga Alkali Zariya da ya yi tawaye ga kungiyar Izala bisa dakatar da shi, amma ya bayyana cewa zai cigaba da mata biyayya.
An ji Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce shugaban nasa ya dauki wannan mataki ne domin ganin abubuwa su lafa ba saboda wani nufi ba.
Ramadan: Malami ya yi nasiha ga Musulmi
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya yi wa Musulmai nasiha game da watan Ramadan.
Malamin ya bayyana cewa yana da muhimmanci kowane Musulmi ya dage da ibada a watan Ramadan, musamman a kwanaki 10 na karshe.
Sheikh Al-Juzuri ya bayyana cewa akwai daren Lailatul Qadr a kwanakin karshen Ramadan, inda ake bukata a tashi a yi sallar dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
