Ganin Fetur Ya Tashi a Duniya, Tinubu Ya Bada Umarnin Gaggawa a Kawo wa 'Yan Najeriya Sa'ida
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a raba kayan sauya injin mota zuwa amfani da iskar gas (CNG) kimanin 100,000 a fadin Najeriya
- Matakin na da nufin rage radadin tashin farashin fetur da ya biyo bayan rikicin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya a sakamakon toshe babbar hanyar sufuri
- Gwamnati na kuma yi shirin gina karin tashoshin cika tankin mota da gas da wuraren cajin motoci masu amfani da lantarki a manyan hanyoyi a Arewa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta rarraba kayan sauya injin mota zuwa amfani da iskar gas (CNG) kimanin 100,000 a duk fadin Najeriya.
Shugaban shirin gwamnatin tarayya na CNG, Ismaeel Ahmed, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 10 ga watan Maris, 2026 bayan wata ganawa da shugaban kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Yakin Amurka da Iran zai rikita duniya, farashin litar fetur zai doshi N2000 a Najeriya

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa Ahmed ya ce umarnin shugaban kasa wani bangare ne na kokarin gwamnati na rage kudin sufuri da kuma fadada amfani da makamashi na daban.
Gwamnatin Najeriya ta dauki mataki kan tsadar mai
A yanzu haka, farashin fetur wanda ya wuce N1,000 a kowace lita tun ranar 7 ga Maris, ya ci gaba da karuwa a wasu jihohi kamar Legas, Ogun da Kaduna.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa za a dauki matakin saukakawa yan kasa ne musamman a lokacin da kasuwar man fetur ta duniya ke fuskantar sauye-sauye sakamakon rikicin da Gabas ta Tsakiya.
Binciken ya kuma nuna cewa hauhawar farashin fetur ya jawo karin kudin mota ga fasinjoji a jihohi da dama, inda wasu hanyoyi kudin sufuri ya ninka sau biyu.
Ismaeel Ahmed ya ce shugaban kasa yana neman karin bayani kan yadda farashin fetur da dizal ke tashi saboda rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Yakin Iran da Amurka ya kara taba Dangote, ya canza farashin fetur karo na 3 a Najeriya
Yadda matakin Tinubu zai taimaki Najeriya
A cewarsa, shugaban ya bukaci a kara yawan gas da CNG a fadin kasar domin rage kudin sufuri ga jama’a.
Ya ce:
“Shugaban kasa yana son sanin abin da muke yi domin kara samar da gas da CNG a dukkan sassan kasa, ta yadda jama’a za su rika biyan kudin sufuri mai sauki."
Ya bayyana cewa a cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa za a fara rarraba kimanin kayan sauya injin mota 100,000 domin bai wa masu motoci da masu keke napep.
Ismaeel Ahmed ya ce cibiyoyin da ake sauya injinan za su yi aiki sosai yayin da ake fara wannan shiri.

Source: Facebook
Shugaban shirin Pi-CNG ya kuma ce shugaban kasa ya ba da umarnin a hanzarta gina kayayyakin more rayuwa na tashoshin cika CNG da wuraren cajin motoci masu amfani da lantarki a fadin Najeriya.
Ya ce gwamnati na ba da muhimmanci musamman ga manyan hanyoyin sufuri a yankin Arewa, kuma ana kan aikin gina tashoshin cika tankunan abubuwan hawa da CNG guda 77 a sassa daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amincewa Yarbawa su dauki 'yan sa kai don kare yankinsu daga 'yan ta'adda
Farashin fetur na hawa a Najeriya
A baya mun wallafa cewa kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta PETROAN ta yi gargadin cewa farashin fetur zai kara hawa daga yadda ya ke a yanzu.
Wannan al'amari ya biyo bayan yakin da aka gwabzawa tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran da aka fara a ranar 28 ga watan Fabarairu, 2026 tare da kashe mutane da dama.
PETROAN ta ce akwai yiwuwar farashin kowace litar man fetur ta kai N2, 000, yayin da farashin dizal ma na iya kusantar N3,000 matukar aka ci gaba da tashin hankalin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng