Iran/Isra’ila: Bama Bamai Sun Hana ’Yan Najeriya Sakat, Ana Kokarin Tsamo Su
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana kokari da ta ke yi wurin ganin ta kwashe 'yan kasar da suka makale a Gabas ta Tsakiya
- Ta ce tana kokarin dawo da ‘yan Najeriya da suka gaza samun damar fitowa a Iran da Qatar sakamakon rikicin yankin
- Ma’aikatar harkokin waje ta ce ana fuskantar kalubalen sufuri da sharuddan shiga Armenia wajen fitar da ‘yan Najeriya daga Iran
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tana kokarin tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya da suka makale a Gabas ta Tsakiya.
'Yan Najeriya da dama na makale a kasashen Qatar da Iran sakamakon rikicin da ya barke a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa shi ya tabbatar da haka ga wakilin Punch a Abuja.
Abin da gwamnati ke yi wa yan Najeriya
Ebienfa ya ce gwamnatin na bai wa ‘yan Najeriya da ke wuraren da rikici ya fi tsanani fifiko, musamman wadanda ke Iran da kuma Israel.
Ma’aikatar ta ce tana nazarin hanyoyi daban-daban domin taimaka wa ‘yan kasar da abin ya shafa, tare da rokon su da su yi hakuri yayin da ake shirin dawo da su gida.
A cewarsa, wadannan wurare ne da ake fama da hare-haren makamai masu linzami da bamabamai, wanda ya kara wahalar da shirin kwashe mutane zuwa wurare masu tsaro.
Ebienfa ya bayyana cewa fitar da ‘yan Najeriya daga Iran na fuskantar kalubalen sufuri, musamman wajen jigilar su zuwa iyakar Armenia.
Ya ce wasu kamfanonin sufuri a Iran na taka-tsantsan wajen samar da motocin bas da za su dauki daliban Najeriya daga jami’o’i zuwa iyakar Armenia.
Haka kuma ya ce hukumomin Armenia sun gindaya sharadi cewa duk wanda zai shiga kasarsu dole ne ya nuna hujjar tikitin fita daga kasar.
Ebienfa ya kara da cewa gwamnati na duba hanyoyin tallafa wa daliban da suka makale, ciki har da samar musu da abinci, kudaden gaggawa da kuma tufafin sanyi saboda yanayin sanyi.

Source: Twitter
Matsalar da 'yan Najeriya suka samu
Game da ‘yan Najeriya da suka makale a Doha a Qatar, Ebienfa ya ce yawancinsu fasinjojin wucewa ne da jiragensu suka samu tangarda.
Ya ce kamfanin jirgin sama na 'Qatar Airways' ya samar masu da masauki a otal otal tare da abinci sau uku a rana.
A cewarsa, jami’an ofishin jakadancin Najeriya a Doha sun ziyarci ‘yan Najeriya da suka makale domin karfafa musu gwiwa da kuma duba hanyoyin da za a dawo da su gida.
Ya kara da cewa daya daga cikin hanyoyin da ake tunani ita ce dawowar wasu jiragen Qatar kadan-kadan, wanda idan aka saka Najeriya a cikin wuraren da za su je, hakan zai taimaka wajen dawo da ‘yan Najeriya gida.
Najeriya ta tsoma baki a rikicin Iran/Isra'ila
An ji cewa Gwamnatin tarayya ta fitar da gargadin tsaro ga ’yan Najeriya mazauna Iran da kasashen Gulf ana tsaka da rigima.
Wannan sanarwa ya biyo bayan kai hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran da ya tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce tana sa ido kan rikicin da ke kara kamari, tare da shawartar jama’a su guji wuraren sojoji da taruka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


