ICPC: Lauyan El Rufa'i Ya Yi Martani kan 'Gano' Gidajen Tsohon Gwamna a Kasar Masar
- Lauyan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya zargi ICPC da yin abin da ya kira tsangwamar siyasa
- Ya ce rahotannin da ke cewa El-Rufai na da kadarorin biliyoyin Naira a Masar magana ce kawai da zummar ci gaba da rike shi
- Lauyan ya ce tsare 'dan siyasar sama da kwanaki 20 ba tare da tuhuma ba ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Lauyan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, Ubong Esop Akpan, ya zargi ICPC da gudanar da abin da ya kira tsangwamar siyasa a kan tsoron gwamna.
Ubong Esop Akpan ya yi wannan bayani ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa El-Rufai na da kadarori na biliyoyin Naira a kasar Masar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wadanda aka ce an gano su ne yayin binciken da hukumar ke yi kan shekarun da ya yi yana gwamna.
Lauyan Nasir El-Eufa'i ya dura kan ICPC
Daily Post a wallafa cewa wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan 2026 Akpan ya bayyana zarge-zargen da cewa ba su da tushe ko makama.
Ya kara da cewa rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai sun dogara ne da majiyoyin da ba a bayyana sunayensu ba, kuma ba su da wata hujja mai tabbaci da za a iya tantancewa.

Source: Twitter
Lauyan ya kuma ce zarge-zargen wani bangare ne na abin da ya kira shirye-shiryen bata suna da aka tsara domin bata sunan El-Rufai a idon jama’a.
A cewarsa, manufar irin wadannan rahotanni na jawo goyon bayan jama’a domin ci gaba da tsare tsohon gwamnan.
Lauyan El-Rufa'i ya dura kan EFCC
Akpan ya bayyana cewa tun daga daren ranar 18 ga Fabrairu, 2026 ne ake tsare da El-Rufai, bayan wasu jami’an tsaro dun damka shi a hannun hukumar EFCC.
Ya ce kafin hakan, tsohon gwamnan ya mika kansa ga EFCC da kansa a ranar 16 ga Fabrairu domin amsa tambayoyi, kuma daga baya aka ba shi beli na wucin gadi kafin a mayar da shi ga ICPC.
Lauyan ya ce ci gaba da tsare shi sama da kwanaki 20 ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba ya saba wa sashe na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Akpan ya kuma bayyana shakku a kan sahihancin umarnin tsarewa na kwanaki 14 da aka ce wata kotun majistare ta bayar a ranar 19 ga Fabrairu.
Ya kara da cewa umarnin ya kare ne a ranar 4 ga Maris, kuma ba a taba mikawa El-Rufai ko lauyoyinsa ba.
An gano kadarori masu alaka da El-Rufa'i
A baya mun wallafa cewa hukumar ICPC ta gano wasu manyan kadarori a ƙasar Masar da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Rahotanni sun nuna cewa an sayi kadarorin ne tsakanin shekarun 2021 zuwa 2023 a wasu unguwanni masu tsada da gine-ginen alfarma na New Cairo.
Ana binciken gidajen alfarmar da gidajen haya da dama a wurare irin su Arabella Estate, Banafsek Estate, Oriana Estate da Cairo Festival City da aka danganta da El-Rufa'i.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


